Ƴan Chelsea na jinya a shirin wasa da Copenhagen - Maresca

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta ɗan ci karo da koma baya, sakamakon da ƴan wasanta ba lafiya a shirin da take na buga Conference League da FC Copenhagen in ji Enzo Maresca.
Ƙungiyar Stamford Bridge za ta karɓi bakuncin Copenhagen a gasar zakarun Turai ranar Alhamis karawa ta biyu zagayen ƴan 16.
Chelsea ce ta je Denmark ta yi nasarar cin 2-1 a wasan farko a makon jiya.
Ƴan wasan Chelsea da ba su samu yin atisaye ba a makon nan sun haɗa da ƙyaftin, Reece James da Cole Palmer da kuma Christopher Nkunku.
Ranar Lahadi Chelsea ta yi nasarar cin Leicester City 1-0 a Premier League a Stamford Bridge.
''A karon farko Cole da Reece da Christopher sun motsa jiki.'' in ji Maresca.
''Sun ɗan ci karo da cikas, Amma yanzu sun murmure, A jiya ba su yi atisaye ba da kwana biyu da suka wuce.''
Chelsea ta lashe dukkan wasa bakwai a Conference League kawo yanzu da cin ƙwallo 28 aka zura mata shida a raga.
Haka kuma Maresca ya tabbatar da cewar Chelsea za ta yi wasan na ranar Alhamis ba tare da Malo Gusto da Marc Guiu da Nicolas Jackson da kuma Noni Madueke.
Idan Chelsea ta kai zagayen ƙwata fainal za ta fuskanci ko dai Molde ko kuma Legia Warsaw.












