Barcelona ce kaɗai ta ci wasa huɗu a jere da fara La Ligar bana

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Barcelona tana mataki na ɗaya a kan teburin La Liga da maki 12, bayan lashe wasa huɗu da fara kakar bana.

Mako mai zuwa za a buga wasannin kasa da kasa a jadawalin Fifa, inda ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama ta haɗa maki 12 daga karawa huɗun da ta yi.

Barcelona ta fara da doke Valencia da Rayo Vallecano a gidajensu, sannan ta yi nasara a kan Athletic Club da na Real Valladolid a gidanta.

Wannan shi ne karo na bakwai da Barcelona ta fara da lashe dukkan karawa huɗu da fara La Liga - na baya-bayan nan shi ne a 2018/19.

Haka kuma kakar 2024/25 ita ce ta biyu da ta ci ƙwallaye da yawa 13 aka zura mata uku a raga a fafatawa huɗun da ta buga.

Tazarar ƙwallo 10 a bana ya haura ƙwazon 2009/10 karkashin Pep Guardiola da 2014/15 a jagorancin Luis Enrique da 2018/19 karkashin Ernesto Valverde da tazarar rarar ƙwallo ɗaya kowanne.

Cikin waɗanda suka ci wa Barcelona ƙwallayen a bana sun haɗa da Robert Lewandowski da Lamine Yamal da Pedri da Dani Olmo da Raphinha da Kounde da kuma Ferran Torres.

Lewandowski ya ci mata huɗu, sai ɗan Brazil, Raphinha biye da shi wanda ya ci uku rigis a karawar da Barcelona ta caskara Valladolid 7-0.

Lamine Yamal yana cikin masu haskakawa a bana a Barcelona, wanda ya bayar da ƙwallo huɗu aka zura a raga.

Masu biye da Barcelona a teburin La Liga sun haɗa da Real Madrid da Atletico Madrid da kuma Villarreal da kowacce keda maki takwas.

Barcelona za ta je gidan Girona ranar Lahadi 15 ga watan Satumba, domin buga wasan mako na biyar a La Liga.

Sakamakon wasa huɗu da Barcelona ta lashe a bana

Ranar Asabar 17 ga watan Agusta 2024

  • Valencia 1 - 2 Barcelona

Ranar Asabar 24 ga watan Agusta 2024

  • Barcelona 2 - 1 Ath Bilbao

Ranar Talata 27 ga watan Agusta 2024

  • R. Vallecano 1 - 2 Barcelona

Ranar Asabar 31ga watan Agusta 2024

  • Barcelona 7 - 0 Valladolid