Me ya sa ƙasashen Afirka ke rige-rigen harba tauraron ɗan'adam?

Ƙaddamar da tauroron ɗanAdam da aka harba a sansanin harba tauraron ɗan'adam na Vandenberg da ke California.

Asalin hoton, SpaceX

Bayanan hoto, A watan Agusta Senegal ta harba tauraron ɗan'adam ɗinta a sansanin SpaceX.
    • Marubuci, Chris Baraniuk
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology Reporter
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zuwa yanzu, ƙasashen Afirka 17 sun harba tauraron ɗan-adam sama da 60.

Da Senegal da Djibouti da Zimbabwe duk sun harba tauraron ɗan-adam ɗinsu a cikin wannan shekarar. Sannan ana sa ran wasu gomman ƙasashen Afirka za su harba nasu.

Amma duk da haka, babu sansanin harba tauraron ɗan'adam ko ɗaya a nahiyar.

Bayan haka, manyan ƙasashen duniya suna amfani da sha'awar shiga ɓangaren da ƙasashen Afirka ke yi domin ƙulla alaka da faɗaɗa ƙarfinsu a nahiyar.

Amma shin wasu ƙasashen Afirka za su iya samun damar samun tauraron ɗan-adam ɗinu a falaki?

"Yana da kyau ƙasashen Afirka su shiga fasahar tauraron ɗan-adam sosai," in ji Mista Sumah, inda ya nanata cewa hakan zai taimakawa ƙasashen wajen kula da fasahohinsu da sauƙin samun bayanai.

Bayanan ne za su taimaka wa ƙasashe Afirka a noma da gano barazanar ambaliya da ƙara inganta fasahar sadarwa a ƙauyuka.

Kwaku Sumah, a tsaye a gaban wani farantin aika-saƙon rediyo

Asalin hoton, Kwaku Sumah

Bayanan hoto, Sauƙin harba taurarin ɗan-adam ya ba ƙasashen Afirka damar shiga ɓangaren a dama da su in ji Kwaku Sumah

Amma har yanzu a Afirka ana ganin kamar fasahar tafiya duniyar wata "fasaha ce ta manyan ƙasashe" in ji Jessie Ndaba, manajan darakta na kamfanin Astrofica Technologis, kamfanin fasahar sararin samaniya na Afirka ta Kudu da ke haɗa tauraron ɗan-adam, inda ta ce "kasuwancin kamfaninta yana koma-baya," inji ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

La'akari da barazanar da nahiyar ke fuskanta na sauyin yanayi, fasahar tauraron ɗan-adam zai taimaka wajen inganta albarkatun noma, in ji ta. "Yana da kyau mu fahimci matsalolin da suke damunmu a Afirka, sannan mu lalubo hanyoyin magance su."

A wajen Sarah Kimani, wadda ke aiki a sashen kula da sauyin yanayi na Kenya, ta ce fasahar tauraron ɗan-adam ta taimaka mata da sauran abokan aikinta wajen gano sauyin yanayi da matsalolin da za su auku cikin sauri.

A ƙarshen wannan shekarar ce ita da abokan aikinta suka fara samun alƙaluma daga kamfanin Eumetsat spacecraft, waɗanda za su taimaka wajen gano yanayin dabbobin daji da tsawa.

Sauyin yanayi yana jawo barazana da matsaloli ba shiri ba tsammani - yawanci kamar tsawa da mummunan fari. "Tsanantar waɗannan bala'o'in suna sauyawa," in ji Ms Kimani, inda ta ƙara da cewa samun alƙaluma a kai a kai, kamar duk minti biyar ko ƙasa da haka zai taimakawa masana sauyin yanayi a nan gaba, da ma sauran ƙasashen Afirka.

"Ƙasashen Afirka ne suka san matsalolinsu, da abubuwan da suke buƙata," in ji Ms Kimani.

Sarah Kimani, ma'aikaciyar sashen sauyin yanayi na Kenya a gaban wani taswirar sauyin yanayi.

Asalin hoton, Sarah Kimani

Bayanan hoto, Kenya za ta amfana idan ta samu ƙarin tauraron ɗan-adam ɗinta in ji Sarah Kimani

Yanzu haka, shirye-shiryen tauraron ɗan-adam na ƙasashen Afirka suna ta'allaƙa ne da ƙasashen waje da masanansu, in ji Temidayo Oniosun, manajan darakta na kamfanin Space in Africa.

Wasu ƙasahen sun tura ɗalibai da injiniyoyi zuwa ƙasashen waje domin ƙwarewa a fasahar tauraron ɗan-adam. "matsalar ita ce, idan sun dawo, zai kasance babu ɗakunan gwaji da sauran kayayyakin aikin da suke buƙata," in ji Mr Oniosun.

Ƙwararru na ƙasar Senegal ne suka haɗa tauraron ɗan-adam na ƙasar, amma duk da cewa ba za a ɗauke musu nasarar da suka samu ba, sai dai yana kyau a bayyana cewa an samu nasarar ce tare da haɗin gwiwar wata jami'a a Faransa, sannan an harba tauraron ɗan-adam ɗin ne da injin harba tauraron ɗan-adam na SpaceX Falcon 9 a California.

Wani farantin aika saƙo na rediyo a birnin Addis Ababa. A ranar Juma'a ce Ethiopia ta ƙaddamar da tauraron ɗan-adam ɗinta na farko mai suna ETRSS-1 domin inganta harkokin noma da rage illar fari.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasar Ethiopia tana fata fasahar tauraron ɗan-adam ɗinta zai taimaka wajen inganta harkokin noma da rage illar fari

Ƙasashen Turai da China da Amurka duk suna ta ƙara shiga shirye-shiryen ƙasashen Afirka na tauraron ɗan-adam. Hakan ya sa an samu cigaba, sannan ya zama hanyar "dogaro wajen gyara diflomasiyya," in ji Mista Oniosun.

Masana suna bayar da shawarar cewa shirye-shiryen sararin samaniya bai kamata su tsaya a kan harba tauraron ɗan-adam zuwa sararin samaniya ba kawai - kasancewar ƙasashen duniya suna amfani da fasahar wajen kece-raini.

Mista Sumah ya ce, "za mu iya shiga cikin yadda ƙasashen gasa domin cin wata ribar daban," in ji shi.

Amma kuma akwai wasu damarmakin, in ji Dokta Delaware Klinger, inda ya ce shirye-shiryen sararin samaniya daga nahiyar - wanda ba ya buƙatar shan fetur sosai - na da kyau, wanda hakan ke nufin ƙasashen Afirka za su taka rawa sosai nan da wasu gomman shekaru masu zuwa a ɓangaren.

Za a iya sake gyara cibiyar sansanin sararin samaniya na Luigi Broglio Space Center, wanda Italiya ta gina a gaɓar tekun Kenya, wadda tun a shekarun 1980s ne rabon da a harba tauraron ɗan-adam a cibiyar.

Lallai nan da wani lokaci za a fara ganin ci gaba a fasahar sararin samani a ƙasashen Afirka. "Yanzu akwai taurorin ɗan-adam da ake aiki a kansu sama da 80 na ƙasashen Afirka," in ji Mista Oniosun. "Gaskiya nan gaba ɓangaren zai ƙara faɗaɗa da samun ƙarin karbuwa."