Arsenal ta je ta kara gwada wa Tottenham ƙwanji a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Arsenal ta haɗa maki uku a gidan Tottenham a wasan mako na huɗu a Premier League da ta yi nasara 1-0 ranar Lahadi.

A wasan na hamayya sun yi minti 45 ba tare da cin ƙwallo, bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu ne Gunners ta ci ƙwallo ta hannun Gabriel Magalhaes.

Karo na 23 da Arsenal ta zura ƙwallo a raga ta kwana har da bugun fenariti tun daga fara kakar bara.

Haka kuma ƙwallo uku ta zura a raga daga wasa huɗu a baya a Premier League da ta fuskanci Tottenham da kai ta ci.

An raba katin gargaɗi bakwai kafin hutu a wasan na hamayya na ƙungiyoyin Arewacin Landan, inda aka bai wa Tottenham biyar da Arsenal biyu, shi ne mafi yawa a minti 45 a Premier League.

Kyaftin Martin Odegaard na jinya da Declan Rice na hutun jan kati, karon farko da ba su buga wa Gunners tamaula tare da a ƴan wasa 11 da take fuskantar ƙungiya tun bayan da suka fara tamaula tare.

Da wannan sakamkon Gunners ta hada maki 10 a wasa huɗu a Premier League, ita kuwa Tottenham tana da huɗu.

Arsenal za ta je gidan Atalanta a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba.

Daga nan Gunners za ta je Etihad, domin fafatawa da Manchester City a karawar mako na biyar a Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Satumba.

Ita kuwa Tottenham za ta ziyarci Coventry a League Cup ranar Laraba 18 ga watan Satumba daga nan ta karɓi bakuncin Brentford ranar Asabar 21 ga watan Satumba a Premier League.

Haɗuwa tsakanin Tottenham da Arsenal

Kafin karawar ta ranar Lahadi, an buga wasa 195 tsakanin ƙungiyoyin da ke Arewacin Landan, Totttenham ta yi nasara 61, Arsenal ta ci 82 da canjaras 52.

Wasan da Tottenham ta yi nasara daga takwas a baya shi ne 3-0 a gida cikin watan Mayun 2022, wadda ta yi rashin nasara biyar da canjaras ɗaya.

Haɗuwa tsakanin ƙungiyoyin biyu an yi fenariti 26 da cin 24 daga ciki, mafi tarihi a Premier League.

Ƙwazon Tottenham

Tottenham ta yi rashin nasara ta biyu da fara wasa huɗu a bana, karon farko kenan tun bayan 2011-12 karkashin Harry Redknapp.

Ƙungiyar ta yi rashin nasara bakwai daga wasa 11 a baya a Premier League da cin karawa uku da canjaras ɗaya.

Tun farko saura ƙwallo ɗaya da Son Heung-min ke bukata ya zura a raga, ya shiga jerin ƴan wasa 20 da suka zura 122 a raga a Premier League.

Dwight Yorke da kuma Raheem Sterling kowanne ya ci ƙwallo 123, suna mataki na 19 a jerin masu cin ƙwallaye a gasar.

Ƙwazon Arsenal

Arsenal ta yi nasara 10 daga wasa 11 da ta buga a waje da canjaras ɗaya daga ciki wasa tara ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba.

An kawo karshen wasa takwas da Gunners ta yi a jera tana nasara, bayan da ta yi 1-1 da Brighton a karawar mako na uku.

A kakar bara a Premier League, Bukayo Saka ya ci Tottenham gida da waje.

Da ace ya zura ƙwallo a raga ranar Lahadi, da ya zama na uku da zai ci ƙwallo karo na uku a wasan hamayyar, bayan Emmanuel Adebayor da kuma Robert Pires.

Raheem Sterling ya zama na farko a matakin sabon ɗan wasa da ya buga wasan hamayya, tun bayan Isaiah Rankin a Disambar 1997.

Sterling, wanda ya koma Arsenal a bana, ya canji Gabriel a wasan na hamayya ranar Lahadi.

David Raya ya cika shekara 29 da haihuwa a wasan na hamayya, wanda ya tsare ragar Arsenal.