Barcelona ce kan gaba a cin ƙwallaye a raga a La Liga

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Barcelona ce kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a kakar nan mai 59 kawo yanzu, bayan da aka kammala wasannin sati na 21 a karshen mako.

A ranar Lahadi Barcelona ta caskara Valencia da cin 7-1 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka kara.

Waɗanda suka ci wa Barcelona ƙwallayen sun haɗa da Frenkie de Jong da Ferran Torres da Raphinha da Fermín López da ya ci biyu da Robert Lewandowski da kuma César Tárrega da ya ci gida.

Sai dai Valencia ta zare ɗaya ta hannun Hugo Duro, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu a fafatawar.

Kenan Barcelona ta ci ƙwallo 59 kawo yanzu an zura mata 24, mai maki 42 a mataki na ukun teburi kakar bana.

Real Madrid ce ta biyu da ta ci ƙwallo 50 aka zura mata 20, mai maki 49 ta daya a kan teburin La Liga.

Villareal ce ta uku mai ƙwallo 39 aka zura mata 32 a raga mai maki 34 ta biyar din teburin bana.

Jerin masu yawan ƙwallaye a raga a La Liga:

  • Lewandowski Barcelona 17
  • Mbappé Real Madrid 15
  • Raphinha Barcelona 12
  • Budimir Osasuna 10
  • Lukébakio Sevilla 9
  • Júnior Real Madrid 8
  • García Deportivo Alaves 8
  • Sørloth Atletico 8
  • Pérez Villarreal 8
  • Bellingham Real Madrid 7

Wasannin mako na 23 da za a buga a La Liga:

Ranar Juma'a 31 ga watan Janairu

  • Leganes da Rayo Vallecano

Ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu

  • Getafe da Sevilla
  • Villarreal da Real Valladolid
  • Atletico Madrid da Mallorca
  • Espanyol da Real Madrid

Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu

  • Barcelona da Deportivo Alaves
  • Valencia da Celta Vigo
  • Osasuna da Real Sociedad
  • Real Betis da Athletic Club

Ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu

  • Girona da Las Palmas