Liverpool ta kori kociyanta

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta kori kociyanta, Matt Beard, yayin da ƙungiyar take matsayi na bakwai a teburin babbar gasar mata ta Ingila, wato Women Super League, inda hakan ya kawo ƙarshen aikinsa karo na biyu a ƙungiyar.
Kociyan mai shekara 47, wanda ya ci kofin gasar har sau biyu a lokacin aikinsa na farko, ya sake kama aiki da ƙungiyar a karo na biyu a 2021 kuma ya yi nasarar sake mayar da su zuwa babbar gasar a kakarsa ta farko.
A bara ƙungiyar ta Liverpool ta gama a matsayi na huɗu amma kuma a yanzu suna tsakiyar teburin gasar da tazarar maki tara tsakaninta da ta ƙarshen tebur Crystal Palace.
Ƙungiyar ta yaba masa kan irin gudummawar da ya ba ta wajen nasarorin da ta samu, a wata sanarwa da ta fitar ta raba gari da shi.
"Burinmu shi ne mayar da ƙungiyar inda take kuma gaba ɗayanmu mun cimma haka a 2022 inda suka samu komawa babbar gasar ta mata ta Ingila,'' in ji ƙungiyar.
"Muna buƙatar ɗorawa a kan wannan nasara kodayake hakan yana da wuya, amma mun yi amanna hakan za ta ba mu kyakkyawar damar nasara a filin wasa,'' a cewar ƙungiyar.
A yanzu Liverpool ta naɗa Amber Whiteley a matsayin kociyan riƙon-ƙwarya, yayin da ta shiga neman wanda za ta naɗa na dindindin.
Beard ya jagoranci Liverpool ta ɗauki kofin babbar gasar ta mata ta Ingila sau biyu a jere a 2013 da kuma 2014 a lokacin aikinsa na farko.
Ya bar Liverpool a 2016 inda ya koma ƙungiyar Boston Breakers ta gasar mata ta Amurka, (National Women's Soccer League), to amma ya yi shekara ɗaya ne kawai a Amurka ya sake komawa Ingila inda ya zama kociyan ƙungiyar West Ham ta mata.
Bayan shekara biyu da Hammers da kuma aikin riƙon-ƙwarya a Bristol City, Beard ya sake komawa Liverpool a 2021.
Casa Liverpool da Manchester City 4-0 a ranar 16 ga watan Fabarairu ya kasance wasa na ƙarshe da kociyan ya jagorance ta, kasancewar ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasanninta bakwai a cikin 14 na gasar a kakar nan.












