Yadda tiyatar sauya kamanni ke samun karɓuwa a China

- Marubuci, Natalia Zuo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye, World Service Investigations
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Abbay Wu tana da shekara 14 lokacin da ta fara yin tiyatar sauya halittarta.
Bayan an yi mata maganin wata rashin lafiyar da ta yi fama da ita, nauyin Abby ya ƙaru daga kilogiram 42 zuwa kilogiram 62 a cikin watanni biyu.
Malamin da ke koyar da ita darussan wasan kwaikwayo ya yi la'akari da wannan sauyin da aka samu.
"A lokacin da nake shiryawa jarabawar wasan kwaikwayo, malamina ya ce min a da ni ce tauraruwar wasan kwaikwayo amma kuma yanzu na yi ƙiba sosai inda ya ce ko na bar wasan kwaikwayon kwata-kwata ko na san yadda zan yi na rage ƙiba." in ji Abby.
Abby ta ce maganar da malaminta ya fada mata ta yi matuƙar sanyaya mata gwiwa inda ta kai kuka wajen mahaifiyarta.
Ganin damuwar da ƴar ta shiga, mahaifiyar ta yanke shawarar kai ta asibiti don yi mata tiyatar sauya kamanni inda za a fi mayar da hankali a tumbin Abby da cinyoyinta.
Kalaman da mahaifiyarta tayi mata na cewa "karda ki saka wani tsoro a zuciyarki, idan kika shiga aka yi miki wannan tiyatar, za ki fito a sabuwar mace, kyakyawa,"
shi ne ke ƙarfafa mata gwiwa in ji Abby.
Amma abin da ta fuskanta a lokacin tiyatar ya wuce abin da take tsammani inda ta ce tiyatar ta yi matuƙar girgizata saboda allurar kashe zafin da ake yi mata ba mai sa bacci ba ce, idonta biyu lokacin da ake yi mata aiki.
"Ina ganin iya yawan kitsen da aka ciro daga jikina da kuma yawan jinin da nake zubarwa" in ji Abby, "abu ne mai ban tsoro.".

Asalin hoton, Family handout
A yanzu da take shekara 35, Abby ta yi tiyatar sauya kamanni sama da 100 inda ta kashe rabin dala miliyan.
A yau, Abby na da asibitin yi wa jiki kwaskwarima a tsakiyar Beijing kuma yana ɗaya daga cikin fitattun asibitoci a cikin masu aikin sauya kamanni a China.
Abby ta ce tiyatar da ta yi na ci gaba da janyo mata matsala a jikinta.
A cikin gidanta a Beijing, ta zauna a gaban madubi tana shafa man concealer a kan ciwon da ta samu a allurar sauya kamanni na fuska da tayi na baya-bayan nan - maganin da take yi duk wata domin samun siriri da miƙaƙiyar fuska
Duk da haka, Abby ta ce ba ta da wani nadama. Ta amince da cewa mahaifiyarta ta yanke mata shawarar da ya dace duk a shekarun nan.
"Tiyatar da na yi ta yi amfani sosai, na samu farin ciki da kuma ƙarfin gwiwa a kodayaushe. Tabbas mahaifiyata ba yanke shawarar da ta dace a kaina."

Asalin hoton, Abby Wu
Tiyatar sauya kamanni abu ne da ake ƙi a baya, amma yanzu tiyatar ta samu karɓuwa sosai inda adadin mutanen da ke yin tiyatar suka ƙaru sosai a cikin shekaru 20 da suka gabata a China.
Wannan ya samo asali ne daga ƙaruwar kuɗin shiga na mutane da sauyin ra'ayoyi na al'umma, musamman sakamakon tasirin kafafen sada zumunta.
A kowace shekara, kusan mutum miliyan 20 a ƙasar China ne ke yin tiyatar sauya kamanni inda yawancin su matasa mata ne.
Jinsin mata ne kashi 80 cikin 100 na masu yin wannan tiyatar, kuma matsakaicin shekarun masu yin ta bai wuce 25 ba.
Kodayake 'kyau' ya daɗe yana da muhimmanci a al'adun ƙasar China musamman ga mata, ƙa'idodin abin da ake ɗauka a matsayin 'kyau' suna sauyawa.
A kwanakin nan, ana ƙara yawan bin hanyoyin da suka fi tsanani kuma masu ban tsoro domin cimma wani irin kamanni da ke nuna ƙayatarwa da kuma zai saka tsoho ya yi kama da yaro.

Asalin hoton, TikTok
Manhajojin tiyatar sauya kamanni kamar SoYoung (New Oxygen) da GengMei (More Beautiful) sun ƙara shahara sosai, suna tallata amfani da lissafin kwamfuta wajen tantance abubuwan da ake ɗauka a matsayin "kura-kuran fuska.
Waɗannan manhajoji na duba fuskar mutane, suna nazarin siffofinsu, sannan su ba da shawarwarin tiyatar da za su yi daga asibitoci mafi kusa inda suke samun nasu kason daga kowace tiyata da aka yi.
Abby, ɗaya daga cikin fitattun masu tasiri na farko a fannin tiyatar sauya kamanni a ƙasar China ta bayyana labarinta a fili a shafukan sada zumunta.
Ta shiga SoYoung tun bayan da aka ƙaddamar da shi sai dai, duk da cewa ta yi sama da tiyata 100, manhajar har yanzu na nuna wasu "kura-kurai" a fuskarta.

Asalin hoton, SoYoung
'Kamar da siminti aka yi Fatata'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin biyan buƙatar jama'a da ke ƙaruwa, asibitocin tiyatar sauya kamanni na yawaita a faɗin ƙasar Sin.
Sai dai akwai babban ƙarancin ƙwararrun likitoci, kuma da dama daga cikin waɗannan cibiyoyi na aiki ba tare da lasisi ba.
Rahoton da wani kamfanin bincike mai zaman kansa, iResearch, ya fitar a shekarar 2019 ya bayyana cewa kusan cibiyoyi 80,000 a China na yin ayyukan tiyatar sauya kamanni ba tare da lasisi ba, kuma akwai kusan ma'aikata 100,000 da ke yin tiyata ba tare da cancantar da ta dace ba.
Wannan matsala ta haifar da yawan samun manyan kuskure wajen yin tiyatar.
Dr. Yang Lu, wani ƙwararren likitan tiyatar sauya kamanni wanda ke da lasisi kuma mai mallakar asibiti a birnin Shanghai, ya ce a cikin 'yan shekarun nan, adadin mutanen da ke neman gyaran tiyata sakamakon kuskuren da aka yi musu a baya yana ƙaruwa sosai.
"Na ga mutane da dama da aka lalata musu tiyata saboda sun je wuraren da ba su da lasisi," in ji Dr. Yang.
"Wasu ma har a cikin gidajen mutane aka yi musu tiyatar."

Yue Yue, mai shekara 28, na daga cikin waɗanda tiyatar da suka yi ta lalace da tsanani.
A shekarar 2020, ta yi allurar "baby face collagen" , wadda ake amfani da ita don sanya fuska ta bayyana a cike, a wani asibiti mara lasisi da wata ƙawarta ta buɗe. Amma sinadarin da aka saka mata ya bushe ya kuma yi tauri a fuskarta.
"Fata ta kamar tana da siminti a ƙarƙashinta," in ji ta.
Da ta gaji da ciwon da allurar ta haifar, Yue Yue ta nemi mafita daga a asibitocin da ta samu ta hanyar shafukan sada zumunta.
Wani asibiti ya yi ƙoƙarin cire sinadarin da aka saka mata ta hanyar amfani da allura.
Sai dai maimakon su fitar da sinadarin da ya yi tauri, sai suka cire namanta, abin da ya sa fatarta ta saki.
Wani asibitin kuma ya yi ƙoƙarin ɗaga fatarta kusa da kunnenta domin isa ƙasan inda aka yi allurar, lamarin da ya bar manyan tabo guda biyu a fuskarta
"Dukkan kamanni na ya sauya, ya ruguje. Na rasa hasken da nake da shi, kuma hakan ya shafi aikina," in ji Yue Yue.
A bara, ta gano Dr. Yang ta manhajar SoYoung, kuma tun daga lokacin ta yi tiyatar gyara har sau uku.
Ko da yake tiyatar Dr. Yang ta inganta halin da take ciki, akwai yiyuwar wasu daga cikin illolin da tiyatar baya ta haifar ba za su daina ba har abada.
'Aikina ya lalace'
A kowace shekara, dubban mutane kamar Yue Yue na fāɗawa hannun asibitocin tiyatar sauya kamanni marasa lasisi a ƙasar China.
Amma kuma wasu daga cikin asibitocin da ke da lasisi da likitocin da ke da ƙwarewa ba sa bin ƙa'idoji yadda ya kamata.
A shekarar 2020, tiyatar gyaran hancin da aka yi wa jarumar fina-finai Gao Liu ta lalace, inda hancin nata ya fara baƙi har ya lalace, lamarin da ya yaɗu sosai a shafuan sada zumunta.
"Fuskata ta lalace ƙwarai kuma hakan ya sa nake cikin baƙin ciki. Wannan ya lalata min aikina na fim gaba ɗaya," in ji Gao Liu.
Ta yi tiyatar gyaran hanci a wani asibitin da ke da lasisi a Guangzhou mai suna 'She's Times', a hannun wani likita mai suna Dr. He Ming, wanda aka bayyana a matsayin babban likita kuma ƙwararre a tiyatar gyaran hanci.
Sai dai a gaskiya, Dr. He bai da cikakkiyar cancantar yin irin wannan tiyatar ba tare da kulawar wani ba, kuma bai samu lasisin likitan tiyatar sauya kamanni daga Hukumar Lafiya ta Lardin Guangdong ba.
Hukumomi sun ci tarar asibitin, wanda daga bisani ya rufe bayan hargitsin, sannan suka dakatar da Dr. He daga aiki na tsawon wata shida.
Amma makonni kaɗan kafin a rufe 'She's Times' wani sabon asibiti mai suna 'Qingya' ya nemi rijista a daidai wannan adireshi.

Asalin hoton, Gao Liu
BBC Eye ta gano dangantaka mai ƙarfi tsakanin She's Times da Qingya, kamar amfani da asusun Weibo ɗaya da kuma ci gaba da aiki tare da wasu daga cikin ma'aikatan 'She's Times, ciki har da Dr. He.
BBC ta kuma gano cewa Dr. He ya samu lasisin likitan tiyatar sauya kamanni a watan Afrilu na 2024, kodayake a gaskiya an hana shi neman wannan lasisi na tsawon shekara biyar daga lokacin da aka hukunta shi a shekarar 2021.
A yanzu Qingya na iƙirarin cewa ta buɗe rassan guda 30.
Dr. He, Qingya, da Hukumar Lafiya ta Lardin Guangdong ba su amsa buƙatar BBC ta neman ƙarin bayani ba.
Ofishin Jakadancin China a Birtaniya ya ce: "Gwamnatin China tana buƙatar kamfanoni su gudanar da aikinsu cikin cikakken bin dokokin ƙasa da ƙa'idoji, da manufofin da suka dace."
Bayan shekaru huɗu da kuma tiyatar gyara guda biyu, hancin Gao Liu har yanzu bai daidaita ba.
Hukumar Lafiyar China na ƙoƙarin daƙile matsalar rashin ƙwararrun ma'aikatan lafiya da ke yin aikin da ya wuce ƙwarewarsu a cikin 'yan shekarun nan - ciki har da umartar hukumomin lafiya na cikin gida su inganta dokoki da kuma fitar da ƙa'idoji mafi tsauri amma kuma matsalar ta ci gaba.











