Me ya sa har yanzu ake aminta da hasashen Nostradamus kan abubuwan da ke faruwa a duniya?

Nostradamus.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nostradamus masani ne ɗan Faransa da yake warkar da marasa lafiya.
    • Marubuci, Global Disinformation Unit
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Bayan mutuwar Fafaroma Francis a wannan makon, sai maganar hasashen ƙwararren mai hasashen ɗan Faransa da ya yi shuhurra a ƙarni na 16, Nostradamus ta dawo.

Ba wannan ba ne karon farko da hasashensa game da abubuwan da suke wakana a duniya suka zama gaskiya.

Amma shin me ya sa har yanzu mutane suke da ra'ayi kan hasashensa har yanzu?

Michel de Notredame, wanda aka fi sani da Nostradamus, likita ne ɗan Faransa wanda ya yi fice wajen warkar da marasa lafiya da annoba ta illata.

Haka kuma mai hasashen abubuwan da za su faru ne wanda ya rubuta littafin Les Prophéties da aka wallafa a shekarar 1555 cikin waƙe.

Littafin ya ƙunshi hasashe-hasashe guda 942, waɗanda a cewarsa suke bayyana abubuwan da za su faru, musamman na abubuwan al'ajabi da bala'o'i'.

Duk da cewa ana ganin hasashen nasa ba su da cikakken bayani, daga cikin waƙoƙin akwai wanda aka yi tunanin ya yi na mutuwar "wani dattijon fafaroma" wanda masu sharhi a kafofin sadarwa da dama suke tunanin da mutuwar Fafaroma Francis yake yi.

Sai dai gomman Fafaroma sun mutu tun daga shekarar 1555, wannan ya sa ake tunanin zai yi wahala a gane alaƙar hasashensa da mutuwar Fafaroma Francis.

Duk da shaharar da yake da ita a tsakanin fitattun mutane, wasu waɗanda ya yi zamani tare da su suna masa kallon sakarai ne kawai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da shaharar da yake da ita a tsakanin fitattun mutane, wasu waɗanda ya yi zamani tare da su suna masa kallon sakarai ne kawai
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ilimin hasashe abin da zai faru wani ilimi ne ba a iya daddalewa a ilimin kimiyya, wanda yake nuna cewa taurari suna da tasiri wajen juya akalar rayuwar ɗan'adam- ilimin ya fara shuhura ne a tsakanin ƙarni na 16.

An samu fitattun masana a ɓangaren, inda suke ba da shawarwari kan komai na rayuwa, ciki har da aiki da kiwon lafiya da sauransu.

Daga cikin fitattun masu hasashen akwai Nostradamus, wanda yake aikin ba da shawara ga mutane tare da bayyana yadda rayuwar mutum za ta kasance musamman ga masu arziki da manyan mutane.

Sai dai bai taɓa samun ƙwarewa a fannin ba, wanda a wancan lokacin ana koya a makaranta, sannan wasu waɗanda ya yi rayuwa da su suna masa kallon sakarai.

Amma duk da haka, kundin waƙoƙinsa na hasashe sun taka rawa sosai a lokacin, inda suka shiga cikin littafan da aka fi saya.

Ƙarni na 16 lokaci ne mai wahalar gaske ga mafi yawan turawa saboda bala'o'in da suka fuskanta na yaƙe-yaƙe da fari da annoba daban-daban.

A daidai lokacin ne hasashe-hasashen Nostradamus suka zama abin nazari domin samun waraka da shirin ko-ta-kwana.

Kamar yadda ake samun mutane masu zuwa wajen ƴan duba a yanzu, magoya bayan Nostradamus a wancan lokacin sun aminta da ayyukansa wajen samun saiti.

Bayan ɗaruruwan shekaru, masoyansa sun ce ai ya yi hasashen abubuwan da suka faru tun a baya, ciki har da yaƙe-yaƙen duniya da bam ɗin nukiliya da ya tashi Hiroshima da Nagasaki, da annobar Covid-19 da sauransu, duk da cewa bai ambaci sunansu kai-tsaye.

An rubuta hasashen Nostradamus ne da wani tsari da za su iya shiga duk wani irin yanayi da ake ciki, in ji Joëlle Rollo-Koster, farfsesan tarihin a Jami'ar Rhode Island.

Amma duk da haka, sunansa da hasashensa sun daɗe suna zama ababen nazari da kwatance.

Bayan kasancewar hasashensa ba su da takamaiman lokaci - yawanci bai faɗi yaushe za su faru ba - littafan da suke fassara hasashen Nostradamus sun ci kasuwa sosai.

Akwai littafansa na Ingilishi kawai sama da guda 100.

Bayan harin 11 ga watan Oktoba, sai kasuwar littafan Nostradamus suka sake tashi, domin mutane da yawa sun ce ai dama ya yi hasashen harin.

Haka kuma wasu sun ce ya yi hasashen mutane za su isa duniyar wata, da hatsarin matafiya zuwa duniyar wata da ma mutuwar Sarauniya Elizabeth II.

Wani mutum yana duba littafin Nostradamus a wani ɗakin sayar da littafi a Bangalore a 18 ga Satumban 2001

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum yana duba littafin Nostradamus a wani kantin sayar da littafi a Bangalore a 18 ga Satumban 2001

A hasashensa kan rasuwar Fafaroma, wasu na fahimtar cewa Fafaroma Francis ne zai zama fafaroma na ƙarshe.

Sai dai wasu masana sun sanya alamar tambaya kan gaskiyar inda aka lalubo rubutun hasashen, inda suke cewa an ƙirƙire su ne domin siyasa.

"Hasashe na da kyau, kuma akwai mutane da suka matuƙar yarda da su," in ji Joseph Uscinski, farfesan kimiyyar siyasa a Jami'ar Miami.

"Wasu lokutan, nishaɗi ne ke jan hankalin mutane har su fara amincewa."

Masana sun ce a wannan yanayin da ake ciki na rashin tabbas, ba abin mamaki ba ne ganin mutane suna ƙara ƙanƙame hasashen Nostradamus.

Dokta Pfeffer ya ce, "Mutane ba su cika jurewa wajen fuskanta tare da magance rashin tabbas ba, kuma an daɗe ana aminta da masu hasashe tun a zamanunnukan baya domin suna taimakon mutane wajen yanke shawara da ɗaukar matakai manya."