Wace ƙungiya ce ta fi yawan ƴanwasa da za su buga kofin duniya a 2026?, Gasar kofin duniya
Manchester City tana da ƴan wasa 19 da za su wakilci kasashensu a gasar cin kofin duniya 2026 da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Daga cikin waɗannan ƴan ƙwallon, huɗu suna daga cikin tawagar Ingila da suka haɗa da mai tsaron raga, James Trafford da mai tsaron baya, Marc Guehi da Nico O'Reilly da kuma John Stones da koci, Thomas Tuchel ke fatan za su taka rawar gani.
Kamar yadda John Stones zai bar Etihad bayan kammala kakar bana, haka shima ƙyaftin ɗin City, Bernardo Silva wanda ya lashe kofuna a ƙungiyar yana kuma ɗaya daga cikin ƴan wasan uku da za su yi wa tawagar Portugal gasar cin kofin duniya tare da Ruben Dias da kuma Matheus Nunes.
Haka kuma Netherlands da Croatia kowacce tana da ƴan ƙwallon City biyu a cikin tawagarta. Tijjani Reijnders da Nathan Aké suna cikin tawagar Netherlands, yayin da Mateo Kovačić da kuma Joško Gvardiol ke wakiltar Croatia.
Sauran ƴan wasan City da za su halarci gasar sun haɗa da Erling Haaland a Norway da Omar Marmoush a Masar da Rayan Cherki a Faransa da Jérémy Doku a Belgium da Rodri a Sifaniya da Rayan Aït-Nouri a Aljeriya da Antoine Semenyo a Ghana da kuma Abdukodir Khusanov da zai buga wa Uzbekistan gasar kofin duniya 2026.

Asalin hoton, Getty Images









