PSG ta ƙulla yarjejeniya da Sancho, Arsenal ta kusa ɗaukar Gyokeres daga Lisbon

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Paris St-Germain ta gama ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaban Ingila mai shekara 24, Jadon Sancho, amma sai ta yi biya £50m da Manchester United ke nema kan ɗan wasan nata (Sports Zone - in French)

United tana neman ɗauko ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 26, Nordi Mukiele ko ɗan wasan tsakiyar Uruguay mai shekara 23, Manuel Ugarte ko kuma ɗan wasan bayan Slovakia mai shekara 29, Milan Skriniar domin cike gurbin Sancho (Express)

West Ham ta fara tattauna zawarcin ɗan wasan bayan Ingila mai taka leda a Manchester United, Aaron Wan-Bissaka kuma ƙungiyarsa ta yi wa ɗan wasan mai shekara 26 farashin £15m (Sky Sports)

Chelsea ta tuntuɓi ɗan wasan gaban Juventus da kuma Italia, mai shekara 26, Federico Chiesa, amma itama Tottenham ta shiga zawarcin (Team talk)

Genoa na ci gaba da zawarcin tsohon mai tsaron gidan Sifaniya, mai shekara 33, David de Gea, wanda rabonsa da bugawa ƙungiyarsa, Manchester United wasa tun a watan Yulin 2023. (Football Italia)

Aston Villa ta yi tayin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester City mai shekara 28, Kalvin Phillips a matsayin aro. (Football Insider, external).

Everton ta ƙulla yarjejeniyar ɗaukar dan wasan bayan Ireland mai shekara 23, Jake O'Brien daga Lyon ta Faransa. (Sky Sports)

Ɗan wasan gefen Crystal Palace mai shekara 21, Jesurun Rak-Sakyi ya zaɓi komawa taka leda a Southampton duk da cewa Leeds na zawarcinsa. (Football Insider)

West Ham ta shirya biyan AS Monaco £29.5m domin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 25, Youssouf Fofana. (L'Equipe - in French)

AC Milan ta kusa kammala cinikin ɗan wasan bayan Brazil mai shekara 25, Emerson Royal daga Tottenham. (Fabrizio Romano)

Arsenal ta kama hanyar ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting Lisbon, Viktor Gyokeres bayan Liverpool ta gaza gabatar da tayi a kan ɗan wasan mai shekara 26. (Team talk)