Tottenham ta ɗauki ɗan wasan Koriya ta Kudu Yang

Yang

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham ta kulla yarjejeniya ɗaukar ɗan wasan Koriya ta Kudu, Yang Min-hyuk daga Gangwon FC.

Dan wasan mai shekaru 18 zai koma Tottenham a watan Janairun 2025, a kan yarjejeniyar da za ta kare zuwa karshen kakar 2030.

Yang, matashin dan wasan Koriya ta Kudu, ya ci ƙwallo takwas a wasa 25 da ya buga wa Gangwon.

A cikin watan Maris ya fara zura kwallon farko a kungiyar, ya zama shi ne matashin dan wasan da ya zura ƙwallo a raga a gasar K League tun 2013.

Yang zai kasance ɗan ƙwallon Koriya na uku da zai koma Tottenham, bayan kyaftin din Son Heung-min da Lee Young-pyo.