Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon shugaba Lula ya lashe zaben shugaban kasa a Brazil
Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda ya kayar da shugaba mai-ci Jair Bolsonaro wanda ya so samun wa'adi na biyu.
Lula ya lashe zaben da kashi 50.83 cikin 100 na dukkan kuri'un da aka kada, yayin da Bolsonaro ya sami kashi 49.17 cikin 100 na kuri'un bayan da aka kidaya kimanin kashi 99 cikin 100 na dukkan kuri'un da aka kada zuwa karfe 11 na dare.
Za a rantsar da sabo shugaban kasar ranar 1 ga watan Janairun shekara 2023.
Wane ne Luiz Inácio 'Lula' da Silva?
Shekaru 20 ke nan tun da Lula ya lashe zaben shugaban Brazil a karo na farko. Lula tsohon ma'aikaci ne na masana'antun da ke samar da karafa kuma shugaban kungiyar kwadago ne.
Ya shahara a shekarun 1970 yayin da ma'aikatan kasar suka riga shiga jerin yajin aiki suna bukatar karin albashi, matakin da ya ci karo da bukatun gwamnatin mulkin soja ta wancan zamanin.
Ya sami darewa karagar mulki ne bayan da ya rika yin yakin neman zaben samar da sauyi ga halin da 'yan kasar ke ciki.
Ya rika zuba kudade masu yawa ga fannoni kamar ilimin jami'a da samar da tallafi ga mabukatan Brazil, lamarin da ya fitar da miliyoyin talakwan kasar daga talauci.
Yadda 'yan Brazil suka karbi nasarar Lula
Sai dai a 'yan shekarun nan ya fuskanci koma baya a rayuwarsa ta siyasa bayan da aka tuhumi jam'iyyarsa da shi kansa Lula da laifukan cin hanci da na rashawa.
An yanke ma sa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara tara bayan wata shari'a da aka yi a 2017.
Sai dai an yi watsi da hukuncin bayan shekaru hudu, amma wannan bai wanke shi a idanun miliyoyin 'yan kasar ta Brazil ba - wadanda ke kallonsa a matsayin wanda bai cancanci rike mukamin shugaban kasa ba.