Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko fitaccen shugaban siyasar Brazil zai kai labari?
A kashi na biyu cikin wadanda ke sahun gaba a neman shugabancin kasar Brazil a zaben da ke tafe, wakiliyar BBC, Katy Watson ta tambayi Luiz Inácio Lula da Silva ko har yanzu bai sauya ba daga wanda ya guirgiza duniya shekaru 20 da suka gabata?
Ba wai arashi ne ba, da Lula ya zabi dajin Amazon a matsayin a sahun gaba a yakin neman zabensa.
Dattijon mai shekara 76, zai fafata da babban abokin hamayyarsa a zaben da 2 ga watan Oktoba 2022, wato shugaba mai ci Jair Bolsonaro, da aka zarga da lalata dajin Amazon.
Lula ya san cewa batun muhalli na daga manyan batutuwan da ya zama ja gaba a gangamin da ya ke yi a birnin Manaus, mafi girma Amazon, ya shaidawa manema labarai ''doron kasa na da matukar muhimmanci, ya na kuma bukatar kulawa daga gare mu".
"Ya kamata mu kula da dazukanmu, da ruwa, da gonaki, abu muhimmi shi ne, kula da al'umarmu saboda sun dade su na fadi tashi, su na bukatar rayuwa mai inganci," in ji shi. "za mu iya kubutar da kasarmu, mu yi tafiya da dagawa."
Lula ya zabi wurin adana tarihi na Amazon, domin ganawa da asalin 'yan Brazil da tattauynawa kan makomar dajin na Amazon.
"Babu wanda zai so maida Amazon wanke hannu ka taba a duniya ba," ya shaidawa mutanen.
"Abin da mu ke son cin moriya daga arzikinmu, shi ne kauda banbancin ra'ayi tsakaninmu." Wadannan kalamai sun sanya an gane tsohon shugaban ya aike da sako ga abokin hamayyarsa sako.
Shugaba Bolsonaro, ya na bakin cikin yadda kasashen duniya ya kamata su daina yi wa Brazil kallon hadarin kaji, da maida su saniyar ware.
Shekaru 20 kenan tun bayan Lula ya zama shugaban kasa a karo na farko.
Tsohon maeri, kuma dan kwadago, ya yi fice lokacin zanga-zangar ma'aikata ta 1970, lokacin da ma'aikatan sukai kiran gwamnati ta kara musu albashi, da kin amincewa da mulkin sojin kasar.
Ya zama shugaban kasa cike da alkawarin sauyi. Ya taimaka kan rage farashin kayayyaki, ya bunkasa fannin ilimi, da magance bakin talauci ga miliyoyin 'yan kasar.
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana lula da cewa "fitaccen dan siyasar da ya yi suna a doron kasa", Lula ya kammala mulki a wancan lokacin inda aka bashi maki 80 cikin 100 na ci gaban da ya kawo.
Ko ka so shi, ko kar ka so shi babu abin da zai sauya, saboda dan siyasa na gaske. Sai dai a 'yan shekarun nan, duk wannan ta kau, lokacin da farin jinin jam'iyyarsa da shi kan shi Lula din suka samu kan su dumu-dumu cikin danbarwar cin hanci da rashawa.
A shekarar 2017, aka yanke masa hukuncin daurin shbekara 9 a gidan kaso. Sai dai an janye hukuncin bayan shekaru hudu, sai dai karon shi da gwamnati a fagen shari'a na nufin ba shi ne mai ceton Brazil ba.
Maimakon haka, miliyoyin 'yan kasar na ma sa kallon bai dace da zama shugaba ba.
Rabuwar kawunan da 'yan kasaer suka samu ya sanya tambayar ta yayya zai gamsar da hukumar zabe ya cancanci zama shugaba.
"Ba za a sake samun mace-mace da kisan gilla irin wanda aka yi wa dan asalin kasar Dom Phillips da dan jaridar Birtaniya Bruno Pereira a dajin Amazon,'' in ji Lula lokacin da akai masa tambaya kan abin da ya faru.
"Ya kama ta mu kawo sauyi a Brazil, ta zama kasa mai ci gaba da ake kare hakkin dan adam. Na yi imanin za mu sauya Brazil, sauyi na nufin samun nagartacciyar gwamnati da za ta lkare muradun 'yan kasa."
Lula ya tattaunawa da Carol Araujo da ke zaune a tsakiyar , uwa ce mai shekara 24 da 'ya'ya 3. Gidanta na kusa da wani kogi.
A lokacin da ake tunkarar karshen damuna, yankin na fama da kazanta da datti, duk inda ka wuce fasassun kwalabe da tsofaffin akwatuna da kwalabe, ga tarin bola.
Kididdigar hukuma ta nuna sama da mutane miliyan 63 ne ke rayuwa cikin bakin talauci, kuma Carol wadda ke zaune a garin Sao Jorge na daga cikinsu.
Ta ce ba ta da tabbacin ko dawowar Lula zai sauya rayuwarsu, "Zan kadawa Lula kuri'a, saboda lokacin mulkinsa ya yi abin arziki, duk da yanzu ba ni da tabbacin zai yi wani abin azo a gani."
"Kasada ce zan yi, na yi ta kokarin samun aiki amma ban samu ba. Dole na samawa 'ya'yana ingantacciyar rayuwa."
Rahotanni sun nuna cewa, Lula ya dogara ne kan tsofaffi a wannan zaben da ke tafe, mutanen da suke iya tunawa da alkhairansa, amma ya san dole ya shawo kan matasan Brazil.
Farfesa Oliver Stuenkel, ta cibiyar Getúlio Vargasa São Paulo ta ce ''Lula ya tsaya takara da yin nasara a sherkarun 1980, a wancan lokacin mai karfin fada aji ne a kasar, sai dai gwagwarmayar da ake yi ta yanzu ta sha banban da wancan lokacin."
Amma ga Beth Ferreira, ta ce ko a jikinta,"Ni fa ina son Lula kamar rai da ajali, Brazil na bukatar shugaba kamar shi, lokacin da ya fara shugabanci a shekarar 2003 Barazil na cikin tsaka mai wuya, kamar dai yanzu. Mu na tsammanin zai gyara kasarmu, ba mu karaya ba."