Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son Harry Kane, Arsenal za ta aro Camavinga, Tuchel na harin Barca ko Madrid
Manchester United na son sayen dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, a wannan bazarar. (Mail)
Chelsea na kara tashi tsaye wajen ganin ta kulla sabon kwantiragi da dan wasanta na tsakiya Mason Mount na Ingila ganin yadda Liverpool ke kokarin janye shi a bazaran nan. (Guardian)
Har yanzu Liverpool na tattaunawa da Roberto Firmino a kan ba shi sabon kwantiragi amma na gajeren lokaci, kuma ga alama dan Brazil din na son zama a kungiyar. (Fabrizio Romano)
Arsenal na sha'awar kulla yarjejeniya ta ban mamaki ta dauko aron dan wasan tsakiya na Real Madrid da Faransa Eduardo Camavinga, domin kara karfafa kungiyar zuwa karshen kakar nan. (Evening Standard)
Manchester United na neman dauko aron dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Marco Reus, bayan da Erik ten Hag ya gana da wakilin dan wasan na Jamus. (Caught Offside)
Da wuya Thomas Tuchel ya karbi aikin horar da Tottenham idan aka neme shi saboda Bajamushen na harin aikin kociyan Barcelona ko Real Madrid ne a nan gaba. (Florian Plettenberg)
A halin da ake ciki kuma kociyan Borussia Dortmund Edin Terzic ya bukaci matashin dan wasan Ingila Jude Bellingham, da ya fito fili ya yi watsi da zawarcin da Real Madrid da Liverpool ke yi masa ya tsaya da kungiyarsa ta Jamus kawai. (Mirror)
Leicester City ta sake gabatar da tayin sayen dan bayan Stoke City Harry Souttar na Australia bayan da kungiyar tasa ta yi watsi da tayin farko na fam miliyan 10. (Mail)
Arsenal ta kusa kammala cinikin matashin dan bayan Spezia kuma dan Poland Jakub Kiwior a kudin da ake ganin zai kai fam miliyan 20. (Sky Sports)
A yunkurin da yaje yi na yin garanbawul kociyan Aston Villa Unai Emery zai rabu da Calum Chambers, wanda daman a Arsenal ma shi ya sallami dan bayan. (Mirror)
Newcastle United na ci gaba da tattanawa da Flamengo domin cimma matsaya a cinikin matashin dan wasan Brazil na gaba Matheus Franca mai shekara 18. (90min)
Chelsea na son dan bayan Lyon Malo Gusto, amma kuma kungiyar na son rike matashin na Faransa har zuwa karshen kakar nan. (L'Equipe - in French)
Kungiyar Salernitana ta Italiya na tattaunawa da wakilin dan wasan Everton Michael Keane kuma tana da kwarin guiwar dan bayan na Ingila zai yarda. (TuttoSalernitana, ta Football Italia)
Matashin dan gaban Club Bruges Antonio Nusa, dan Norway mai shekara 17, zai koma Manchester City nan gaba a sana'arsa ta kwallon kafa, in ji tsohon dan wasan Holland Ruud Vormer. (Het Laaste Nieuws, ta HITC)