Chelsea ta fara ɗaukar matakan ladabtar da Fernandez

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta fara ɗaukar matakan ladabtar da Enzo Fernandez, bayan da ya saka wani bidiyo a kafarsa ta sada zumunta, inda hukumar ƙwallon kafar Faransa ta ce ya ƙunshi ''wakar wariya da kaskanci.''
Ranar Talata hukumar ƙwallon kafar Faransa ta shigar da korafi ga Fifa kan bidiyon, wanda ƴan wasan Argentina ke rera wakar kan Faransa da ƴan wasanta bakar fata.
Ɗan wasan Chelsea, Wesley Fofana, wanda ya buga wa Faransa wasa ɗaya ya saka hoton bidiyon wakar a Instagram da cewar ''wariyar launin fata mara ma'ana.''
Fernandez, wanda aka ɗauka mafi tsada a Ingila kan £107m a Fabrairun 2023 - ya kuma nemi afuwa kan bidiyon mai ɗauke da tawagar Argentina tana murnan lashe Copa America.
Fifa tana bincike kan bidiyon da ƴan wasan Argentina da dama da suka rera wakar, wadda take tuhumar tushen ƴan wasan Faransa bakar fata.
Chelsea tana da ƴan wasan Faransa bakwai da suke bakar fata da suke cikin 11 da suke fara yi mata tamaula da ya hada da Fofana da Axel Disasi da Benoit Badiashile da Lesley Ugochukwu da Christopher Nkunku da Malo Gusto da kuma Malang Sarr.
"Wakar ta ƙunshi kalaman cin zarafi da babu wani uzuri daga kalaman,'' in ji Fernandez.
''“Bana goyon bayan wariya ta kowace fuska tare da ba da hakuri kan yadda aka yi amfani da kalaman a lokacin murnar bikin lashe Copa America.
Hukumar ƙwallon kafar Faransa za ta tuntuɓi ta Argentina kan bidiyon da Fernandez ya saka a kafar sada zumunta, bayan da Argentina ta doke Colombia 1-0 ta lashe Copa America ranar Lahadi.
An tuntuɓi hukumar ƙwallon kafa ta Argentina, domin jin ra'ayinta.
Faransa ta doke Argentina a zagaye na biyu a kofin duniya a 2018 a Rasha, yayin da Argentiina ta yi nasara a kan Faransa a gasar kofin duniya a 2022 a Qatar.










