Liverpool na son Guler, Yoro zai koma Madrid, Man United za ta dakko Zirkzee

An wallafa

Liverpool na sha'awar Arda Guler, Fulham ta koma kan tebur don daukar Trevoh Chalobah, Manchester United ta shirya tsaf domin kawo karshen zawarcin Jarrad Branthwaite.

Liverpool na zawarcin dan wasan tsakiyar kasar Turkiyya Arda Guler daga Real Madrid, mai shekara 19. (Teamtalk)

Fulham ta farfado da sha'awarta ta neman dan wasan bayan Chelsea Trevoh Chalobah mai shekaru 24. (Standard)

Manchester United za ta daina tattaunawa da Everton kan dan wasan bayan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, sai dai idan an rage farashin dan wasan kasa da fam miliyan 70 (ESPN)

Dan wasan bayan Lille Leny Yoro, mai shekara 18, ya fi son komawa Real Madrid kan Liverpool ko Manchester United. (Marca)

West Ham na fargabar dan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 23, zai nemi ya bar kungiyar a bazara. (Football Insider)

Aston Villa ta nemi dan wasan tsakiyar Argentina mai shekara 21, Matias Soule, amma Juventus ta ce ba na siyarwa bane. (Sky Sports)

Chelsea na tattaunawa da Boca Juniors kan cinikin dan wasan bayan Argentina Aaron Anselmino mai shekaru 19. (Athletic)

Manchester United ta shirya tsaf domin fitar da fam miliyan 33.8 don sayan dan wasan Bologna dan kasar Holland Joshua Zirkzee, mai shekara 23. (Telegraph)

Tsohon kocin AC Milan Stefano Pioli na daga cikin masu neman zama kocin Al-Ittihad. (Fabrizio Romano)

Dan wasan tsakiya na Paris St-Germain da Netherlands Xavi Simons, mai shekara 21 ne babban burin Bayern Munich (Bild Sports)

Arsenal ta kai tayin neman dan wasan Fenerbahce na Turkiyya Ferdi Kadioglu, mai shekara 24. (Ajan Spor)