Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NAPTIP ta gargaɗi ƴan Najeriya kan fataucin mutane zuwa Turai
Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP ta yi gargadi mai karfi tare da ankarar da 'yan kasar kan ƙaruwar fataucin mutane ta hanyar yaudarar su da sunan karatu a Turai ko sama musu aikin yi wanda akasari ke faruwa ta shafukan intanet.
NAPTIP ta ce galibin mutanen da ake fitar da su ketare da sunan karatu kyauta ko ƙarkashin wani tallafi ko samar musu aikin yi kan ƙare ne da karuwanci ko rayuwarsu ta shiga cikin uƙuba.
Fataucin mutanen dai abu ne da mahukunta suka jima suna fafutukar murƙushewa a Najeriya, sai dai yayin da ake ganin a baya yaudarar ta baki ce a wannan lokacin masu wannan mugun aiki, sun sauya salo, inda suke amfani da shafukan intanet wajen cimma burinsu.
Hukumar NAPTIP, da ke yaki da fataucin mutane a Najeriya ta ce galibin mutane da ke faɗawa cikin wannan yaudara matasa ne da shekarunsu ke kamawa daga 18 zuwa 20 da ɗoriya.
NAPTIP ta ce ana yaudarar matasan ne da sunan gurbin karatu kyauta ko tallafi a jami'o'in kasashen ketare, ko kuma a yi masu tayin aikin yi, sai dai a ƙarshe sai su ƙare da aikatau ko karuwanci ga mata.
Sannan duk matashin da ya faɗa cikin wannan tarko yana kasancewa cikin yanayi na rashin zabi kuma fitarsa takan kasance da wahalar gaske, kamar yadda Hassan Hamisu Tahir, daraktan ɓangaren shari'a da bayar da kariya na hukumar ta NAPTIP ya tabbatar.
Hukumar NAPTIP ta ce duk da cewa ba ta da alkaluma kan yawan mutanen da aka yaudara ta wannan hanya, amma dai a kusan kullum ana samun nasarar ceto mutanen da suka haɗa da mata da zama.
NAPTIP da ke sake jaddada jan kunnenta ga 'yan Najeriya da burinsu kawai shi ne su je Turai domin samun rayuwa mai inganci, ta ce a yanzu dai ta yi ƙoƙarin fito da shirye-shiryen wayar da kawuna 'yan kasa, inda suke bin kasuwanni, da wajen ibada da jami'o'i, sannan ta shawarci mutane su kasance masu natsuwa da bincike kafin shigar da kansu cikin abin da ka iya ruguza musu rayuwa.