Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubalen da ke gaban Real Madrid a La Liga da Champions League
Real Madrid za ta buga wasu wasanni masu zafi daga yanzu har zuwa hutun da Fifa kan ware, don fafatawa tsakanin ƙasa da ƙasa.
Fifa ta ware wasu lokuta a jadawalin da take tsarawa, don buga ko dai wasannin sada zumunta ko na neman gurbin gasar kofin duniya da sauran su.
Real Madrid za ta buga wasa takwas, shida daga ciki a La Liga da kuma a gasar Champions League, fafatawar zagayen ƴan 16.
Da farko dai Real za ta karɓi baƙuncin Girona a Santiago Bernabeu ranar Asabar a gasar La Liga, wasa ne tsakanin Real, wadda take ta ɗaya a saman teburi da kuma Girona ta biyu.
Kwana uku tsakani, kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta je RB Leipzig, domin wasan farko zagaye na biyu a Champions League.
Bayan nan Real za ta ƙara buga wasa a waje a gidan Rayo Vallecano a gasar La Liga mako na 25 ranar Lahadi 18 ga watan Fabrairu.
Real Madrid za ta karbi bakuncin Sevilla ranar Lahadi 25 ga watan Fabrairu a Santiago Bernabeu, sannan ta ziyarci Valencia ranar 2 ko 3 ga watan Maris.
Daga nan filin Santiago Bernabeu zai karbi bakuncin wasa masu mahimmaci ga Real Madrid a shirin da take na taka rawar gani a kakar bana.
Za ta fara da karbar bakuncin RB Leipzig a Champions League a wasa na biyu zagaye na biyu ranar Laraba 6 ga watan Maris, karawar da za ta fayyace wadda ta kai kwata fainal a gasar ta zakarun Turai ta bana.
Daga nan Real za ta karbi bakuncin Celta Vigo a wasan mako na 28 a La Liga ranar ko dai 9 ko kuma 10 ga watan Maris.
Wasan ƙarshe da za ta yi daga nan a yi hutu na kalandar Fifa, shi ne wanda za ta ziyarci El Sadar, domin fuskantar Osasuna ranar ko dai 16 ko kuma 17 ga watan Maris.
Wasannin da ke gaban Real Madrid:
- Real Madrid da Girona, La Liga mako na 24 ranar 10 ga Fabarairu.
- Leipzig da Real Madrid, Champions League zagayen ƴan 16 ranar 13 ga Fabarairu.
- Rayo da Real Madrid, La Liga mako na 25 ranar 18 ga watan Fabarairu.
- Real Madrid da Sevilla, La Liga mako na 26 ranar 25 ga Fabarairu.
- Valencia da Real Madrid, LaLiga mako na 27 ranar 2/3 ga Maris.
- Real Madrid da Leipzig, Champions League zagayen ƴan 16 wasa na biyu ranar 6 ga watan Maris
- Real Madrid da Celta, LaLiga mako na 28 ranar 9/10 ga watan Maris.
- Osasuna da Real Madrid, LaLiga mako na 29 ranar 16/17 ga watan Maris.