FA ta ci tarar kocin Liverpool £30,000

Klopp da kansa ya ce ya cancanci jan kati saboda yadda ya yi wa mataimakin alkalin wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Klopp da kansa ya ce ya cancanci jan kati saboda yadda ya yi wa mataimakin alkalin wasan
An wallafa

Hukumar FA ta ci tarar kocin Liverpool Jurgen Klopp yuro 30,00 bayan jan katin a wasan da kungiyarsa ta yi nasara a kan Manchester City a ranar 16 ga watan Oktoba.

An kori Klopp daga filin wasa bayan rashin da'ar da ya yi wa mataimakin alkalin wasa, lokacin da aka ki bai wa Mohamed Salah damar dukan da aka yi masa.

kocin ya nemi afuwa kan halayyar da ya nuna bayan an tashi daga wasa.

"Wani abu ne ya dauki hankaline, ba alfahari nake ba. Na cancanci jan kati," a cewarsa.

An tuhumi Klopp da karya dokar FA ta E3, wadda ta bayyana cewa fadawa alkalan wasa magana bai dace ba, wanda kuma yake janyo, wanda zai iya zama barazana da cin zarafi da zagi".

FA ta ce ba za a taba yarda da wannan halayyar da ya nuna ba, bata dace ba, kuma hukumar da ke lura da dokoki ta sa masa takunkumi da shi lokacin sauraron karar.

Amma Liverpool na da damar kalubalantar takunkumin.