Chelsea ba za ta iya biyan de Jong ba, Juventus na sanya ido kan Martial

An wallafa

Dan wasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong zai iya zuwa Chelsea ne kadai idan ya bar kungiyarsa ta Barcelona, sai dai Chelsea din ba za ta iya biyan shi kudin da Manchester United ke da niyyar ba shi ba idan zai koma United din. (Sport - in Spanish)

Shugaban kungiyar Atletico Madrid Enrique Cerezo ya ce bai san ko wane ne ya kirkiri jita-jitar cewa Cristiano Ronaldo zai koma kungiyar ba daga Manchester United domin a cewar sa a halin yanzu wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. (El Partidazo de COPE, via Eurosport)

Newcastle United na nuna sha’awarta ta dauko dan wasan Chelsea dan asalin kasar Jamus Timo Werner mai shekara 26. (Christian Falk, head of football at Bild)

Juventus dai za ta sanya ido kan Werner ko kuma dan wasan Manchester United, Anthony Martial idan ta gaza dauko dan wasa Alvaro Morata daga Atletico Madrid. (Sky Sports)

Yunkurin kungiyar Tottenham na dauko dan wasa Weston McKennie zai iya cin karo da tangarda bayan da abokin wasansa da suke kungiyar Juventus Paul Pogba ya samu rauni a gwiwa. (Mail)

 Chelsea ta fara mayar da hankalinta kan dauko mai tsaron baya na Inter Milan Denzel Dumfries bayan da yunkurinta na sayo Jules Kounde daga Sevilla ke neman ya ci tura. (Evening Standard)

Mai horas da Barcelona Xavi ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba kungiyar ta iya dawo da Lionel Messi ba a halin da ake ciki kasancewar dan wasan na da kwantaragi da Paris St-Germain, sai dai ya ce ba a san yadda hali zai yi ba a nan gaba. (Goal)

Mai tsaron raga na kungiyar Leicester City, Kasper Schmeichel ya amince ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Nice da ke Faransa, sai dai har yanzu ba a kammala amincewa da batun ba kasancewar har yanzu Leicester din ba ta samu wanda zai maye gurbinsa ba. (L'Equipe - in French)

Shugaban Leicester City, Aiyawatt Srivaddhanaprabha ya ce ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta nuna sha’awar daukar dan wasa Youri Tielemans duk kuwa da cewa kwantaraginsa da kungiyar za ta kare ne a kaka mai kamawa. (Metro)

Everton na son ganin ta dauko dan wasan Sporting Lisbon mai shekara 23 Ruben Vinagre, wanda ya rinka yin wasa a kungiyar Wolves. (Liverpool Echo)

Southampton ta nuna aniyarta ta dauko dan wasan Manchester City mai shekara 19 Sam Edozie, wanda ake sa ran zai tafi Bayer Leverkusen(Mail)