Zaben Najeriya na 2023: Ku ba mu labaran abubuwan da suka shafe ku

An wallafa

Muna so mu ji daga gare ku. Labaran da za mu kawo kan zaɓukan Najeriya za su kasance na abubuwan da suka shafe ku ne kuma daga bakinku.

Za mu so mu ba da labaranku. Za mu yi labaran ne kan abubuwan da suka faru da ku a kan muhimman al’amuran ƙasar.

Muna so mu ba da labaran abubuwan da suke da muhimmanci a wajenku. Gamsuwar masu sauraro ce za ta zama ƙashin bayan rahotanninmu – ma’aikatanmu na bincike kan yadda rikice-rikice a Najeriya suka shafi ‘yan ƙasa kamarku.

Labaranku za su iya zama rahotanninmu – idan aka samu cikakken bayani na ainihi, da kuma hira ta musamman da ƙwararru da kuma mahukunta game da al’amura daban-daban. 

Labarai a ɓangarori biyar masu muhimmanci a rayuwar ƴan Najeriya

Labaran da muke so ku aiko mana za su kasance na abin da ya faru da ku ne kan matsalar rashin tsaro ko abin da ya shafi ɓangaren ilimi ko na lafiya ko cin hanci ko tattalin arziki.

Wato muna so mu ji idan akwai wani labari da kuke da shi a waɗannan fannoni da irin tasirin da ya yi muku a rayuwa.

Alal misali, yadda matsalar rashin tsaro ta shafe ku, ko wani abu na harkar lafiya da ya faru da ku da sauran su.

Idan kuka duba ƙasan shafin nan za ku ga fannonin da kuma inda za ku latsa don cike fom ɗin da za ku sanya bayananku.

Danna adireshin da ke ƙasa ku turo mana labaranku. Ba sai kun bayyana sunanku ba idan ba kwa son hakan.

Kar ku manta da sanya bayanan yadda za mu tuntuɓe ku – lambar waya da imel – don ɗaya daga cikin ma’aikatanmu su nemi ƙarin bayani. Kar ku damu:

Za mu ɓoye sirrinku

Ku ba mu labaranku: Ta yaya matsalar tsaro da rikice-rikice ke shafarku?

Wace matsalar rashin tsaro kuka samu kanku a ciki, kama daga tashe-tashen hankula a birane da karkara da satar mutane don kudin fansa da cin zarafi da fashi da makami da rikicin ƙabilanci da faɗan daba?

Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar rashin tsaro.

Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa.

Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.

Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.

Ku ba mu labaranku: Ta yaya matsin tattalin arziki ke shafarku?

Wace matsalar tattalin arziki kuka sami kanku a ciki, kama daga tsadar kayayyaki da yunwa da wahalar man fetur da tsadar hayar gidaje da hauhawar farashi?

Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar tattalin arziki.

Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa.

Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.

Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.

Ku ba mu labaranku: Wace matsala ce kuka ci karo da  ita kan abin da ya shafi ɓangaren ilimi?

Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren ilimi; alal misali tarnaƙi ta ɓangaren ƙarancin kuɗaɗe ko yajin aiki ko matsalar tsaro ko cin hanci ko rashin shugabanci nagari ko ƙarancin kayan more rayuwa ko tsadar kuɗin karatu ko ƙarancin kayan koyarwa ko kuma siyasantar da harkokin Ilimi.

Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren ilimi.

Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.

Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.

Ku ba mu labaranku: Wace matsala ce kuka ci karo da  ita kan abin da ya shafi ɓangaren lafiya?

Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren lafiya; alal misali samun tarnaki ta hanyar amfani da fasaha a harkokin lafiya ko ƙarancin albashi ga ma’aikata ko rashin fasahar sadarwa da ingantattun ayyukan lafiya ko ƙaruwar tsadar kuɗin asibiti ko ƙarancin ma’aikatan lafiya.

Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren lafiya.

Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.

Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.

Ku ba mu labaranku: Ta yaya matsalar cin hanci da rashawa ke shafarku?

Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar cin hanci da rashawa.

Ko a ɓangaren rundunar ƴan sanda ko rundunar soji ko ɓangaren siyasa da ɓangaren ayyukan jin ƙai da sauran ɓangarori.

Ko kun taɓa samun kanku a matsalar da ta shafi cin hanci da rashawa a Najeriya?

Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na abin da ya danganci hakan.