Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku ba mu labaranku: Ta yaya matsalar cin hanci da rashawa ke shafarku?
Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar cin hanci da rashawa. Ko a ɓngaren rundunar ƴan sanda ko rundunar soji ko ɓangaren siyasa da ɓangaren ayyukan jin ƙai da sauran ɓangarori. Ko kun taɓa samun kanku a matsalar da ta shafi cin hanci da rashawa a Najeriya? Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na abin da ya danganci hakan. Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.
Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.