Yarinyar da ta ɓace ta dawo gida bayan shekara tara a Indiya

An wallafa

Bayan shafe shekara tara, Pooja Gaud mai shekara 16 a ƙarshe ta koma wurin mahaifiyarta. Pooja ta ɓata ne tun a ranar 22 ga watan Janairun 2013 a lokacin da take shekara bakwai.

Ta bayyana cewa wasu ne suka ɗauke ta a wajen makarantarsu a birnin Mumbai a Jihar Maharashtra bayan sun yaudare ta da askirin (Ice Cream).

A ranar 4 ga watan Agusta ne aka gano ta bayan ta tsere. Mahaifiyarta Poonam Gaud ta ji daɗi matuƙa sakamakon dawowar ƴarta. "Da na haƙura kan batun gano ƴata. Amma Ubangiji ya taimake ni," in ji ta.

'Yan sanda sun yi zargin Harry D'Souza da matarsa Soni D'Souza ne suka sace yarinyar saboda ba su taɓa haihuwa ba. Tuni ƴan sanda suka kama Mista D'Souza.

Kafin a sace ta, Pooja tana zaune ne da ƴan uwanta maza biyu da iyayenta a wani ɗan ƙaramin gida a wani ƙauye.

A ranar da ta bace, ta tafi zuwa makaranta tare da babban yayanta, amma su biyun sun yi faɗa inda yayan nata ya tafi makaranta ya bar ta a baya sakamakon ya yi latti.

A lokacin ne ake zargin ma'auratan sun sace yarinyar inda suka yi mata alƙawarin saya mata ice cream.

Pooja ta bayyana cewa ma'auratan tun da farko sun kai ta jihohin Goa sai kuma Karnataka a yammaci da kudancin India, inda suka yi mata barazanar azabtar da ita idan ta yi kuka ko kuma ta ja musu magana.

Ta bayyana cewa an bari ta rinƙa zuwa makaranta na taƙaitaccen lokaci amma bayan da ma'auratan suka samu haihuwa, sai aka cire ta daga makarantar inda duka suka koma Mumbai.

Pooja ta ce cin zarafin da suke yi mata ya ƙaru bayan da suka samu haihuwa,

"Suna dukana da belt, su harbe ni, su naushe ni.

"Wata rana sun duke ni da muciya har sai da jini ya soma zuba daga wuyana.

"Suna tilasta ni na yi aiki a gida da kuma aiki a waje tsawon sa'o'i 12 zuwa 24.

Gidan da D'Souza suka zauna bai da nisa da gidan iyayenta - amma ta ce ba za ta gane hanyar ba, ta bayyana cewa a kodayaushe an saka mata ido, ba ta da kuɗi ko waya kuma ba za ta iya neman taimako ba ko kuma ta nemi hanyar gida.

Na sha da ƙyar

Amma wata rana, Pooja ta yi ƙoƙari inda ta ɗauki wayar ma'auratan a lokacin da suke bacci inda ta saka sunanta a YouTube.

Sai ta ga bidiyoyi da hotuna inda ake ambatar cewa an sace ta da kuma lambobin da za ta iya kira. "A lokacin ne na yi ƙoƙarin neman taimako domin na gudu," in ji ta.

Amma sai da ta ɗauki wata bakwai tana ƙoƙarin ba kanta ƙwarin gwiwa ta tattauna da Pramila Devendra mai shekara 35, wadda ma'aikaciya ce wadda ke aiki a gidan da Pooja ke aiki a matsayin ƴar raino.

Nan take Devendra ta amince ta taimaka mata. Ɗaya daga cikin lambar da aka gani a YouTube ɗin da aka kira lambar Rafiq ce, maƙwafcin mahaifiyar Pooja.

Mahaifiyar da ƴarta sun soma magana ne ta hanyar yin waya ta bidiyo.

Mahaifiyar ta ce ta duba wata shaida da ke jikin yarta tun ta haihuwa wadda ita kaɗai ta san da ita, ko da ta ganta sai ta ƙara farin ciki.

"Duk wani shakku da nake da shi ya tafi, na san na gani ƴata," in ji ta.

Ms Devendra ta ji daɗi matuƙa da ta taka rawa wajen dawo da ƴar gida.

Bayan haɗuwarsu, Pooja, da wasu danginta ƙalilan suka kama hanya zuwa ofishin ƴan sanda domin kai koke.

"Na shaida wa ƴan sanda komai. Har na gaya musu inda waɗanda suka yi garkuwa da ni suke," in ji ta.

Wannan ne ya kai ga kama waɗanda ake zargin. Milind Kurde wanda babban sufeto ne a ofishin ƴan sanda a Mumbai, ya shaida wa BBC cewa tuni aka kai wannan lamarin gaba inda ake zargin mutanen da garkuwa da barazana da duka da safarar yara