Ten Hag ya kasa cin wasa uku a jere a karon farko a United

An wallafa

Newcastle United ta ci Manchester United 2-0 a wasan mako na 29 a gasar Premier League ranar Lahadi a St James Park.

Joseph Willock ne ya fara ci wa Newcastle United kwallo, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Saura minti biyu a tashi daga wasan Newcastle ta kara na biyu ta hannun Callum Wilson.

Karo na uku a jere da Ten Hag ya kasa cin wasa a Premier League tun karbar kungiyar a bana, bayan da Liverpool ta ci 7-0 ranar 5 ga watan Maris.

Sai United ta tashi 0-0 da Southampton a Old Trafford ranar 12 ga watan Maris da wanda Newcastle ta ci 2-0 a St James Park.

Sun tashi 0-0 a Old Trafford a Premier League ranar 16 ga watan Oktoban 2022, sannan United ta ci 2-0 ta lashe Carabao Cup ranar 16 ga watan Fabrairun 2023 a Wembley.

Newcastle ta koma ta uku a teburin Premier da maki 50, United ta koma ta hudu itama maki 50 ne da ita.

Ranar Litinin Tottenham wadda take ta biyar mai maki 49 za ta ziyarci Everton a karashen wasan mako na 29.

Newcastle ta hada maki 50 a Premier League a karon farko tun 2011-12, wadda ta kare a mataki na biyar da maki 65 a kakar.

Ranar 5 ga watan Afirilu, United za ta karbi bakuncin Brighton a gasar Premier League a Old Trafford.

A kuma ranar Newcastle za ta ziyarci West Ham United a dai gasar ta Premier League.

Manchester United ta yi rashin nasara hudu ba tare da Casemiro ba a fafatawa takwas a Premier League a kakar nan, idan ka hada da rashin nasara uku a wasa 19 da ya yi mata tamaula.

Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kafin wasan:

Manchester United ta barar da maki a wasa hudu daga shida da ta fuskanci Newcastle a St James Park a Premier League da cin biyu da canjaras biyu aka doke ta biyu.

Newcastle ta ci United 1-0 a St James Park cikin Oktoban 2019, nasarar da kungiyar kenan a wasa tara a baya da canjaras biyu aka doke ta shida.

United ta ci Newcastle sau 14 a Premier League a St James Park, fiye da sauran kungiyoyin gasar a karawar waje.

Newcastle United

Manchester City da Liverpool suka ci Newcastle a lik a gida, tun bayan daukar Eddie Howe a Nuwambar 2021.

Howe ya yi nasara 15 daga 27 a gida da canajaras tara da rashin nasara uku biyu daga ciki a hannun Liverpool.

Howe ya yi nasara a karawa biyu daga 13 da ya fuskanci United a matakin koci a dukkan fafatawa da canjaras uku da shan kashi a wasa takwas.

Manchester United

An zura kwallo 27 a ragar United a manyan wasannin da ta yi a waje, Bournemouth da Nottingham Forest da Leicester sune aka fi yawan zurawa kwallaye fiye da kungiyar Old Trafford.

A watan jiya Liverpool ta ci United 7-0, wasan da aka doke ta daga karawa 16 a lik kenan da yin nasara 12 da canjaras uku.

Watakila United ta kasa zura kwallo a wasa na uku a jere a karon farko tun bayan Fabrairun 2020.