Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza
Kafofin labaran Iran da Saudiyya sun ce shugabannin kasashen biyu sun tattauna a kan batun rikicin Isra'ila da Falasdinawa, a wata tattaunawa ta farko ta wayar tarho tun bayan dawo da huldar diflomasiyya a tsakaninsu.
Sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman sun zanta a kan bukatar kawo karshen abin da Raisi ya bayyana da laifukan yakin da Israil ke aikatawa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ce Riyadh ta jaddada yunkurin goyon bayanta ga Falasdinawa, da kuma bukatar a shawo kan lamarin ta hanyoyi na diflomasiayya.
Yariman na Saudiyya, ya "tabbatar da cewa Masarautar na yin iya ƙoƙarinta wajen tattaunawa da ƙasashen duniya da na yankin Gabas ta Tsakiya domin daƙile wannan yaƙi da ke ruruwa," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ambato.
Kamfanin ya ruwaito Yariman ya jaddada cewa Saudiyya na watsi da duk wani shiri na kai hari a kan fararen hula a ko'ina suke.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 340,000 aka tilastawa barin muhallansu, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren martani ga harin da Hamas ta kai ranar Asabar.
Isra’ila ta hana mutane fita ta ko ina, duk da yake wasu mazauna yankin suka yi nasarar tsallakawa daga Gaza.
Isra’ila ta katse wutar lantarki da ruwan sha.
Sai dai kuma, ƙasashe da ƙungiyoyi na ci gaba da kiran a samar da yanayin kai tallafi cikin Gaza da kuma bai wa ƴan gudun hijira damar ficewa.
Hukumomi a Masar sun ce an fara tattaunawa don ganin an ƙulla yarjejeniyar kai ɗauki ga mutanen da yaƙi ya ritsa da su.
Amurka ma ta ce tana tattaunawa da Isra’ila a kan yadda za ta taimaka wajen kwashe fararen hula daga Gaza, bayan shafe kwana biyar jiragen yakin Isra’ilan na luguden wuta.
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce dole ne a ba da damar shiga da muhimman kayan buƙatun rayuwa ga mutanen Gaza.
Scott Paul na ƙungiyar ba da agaji ta Oxfam ya ce abubuwan da ke faruwa a Gaza ba su da daɗin ji.
Ya ce ‘’fatanmu shi ne masu faɗa-a-ji, a duniya za su saurari muryoyin mutanen da lamarin ya ritsa da su, su kuma dubi hotunan da suka bayyana na irin wahalar da ake ciki.
Yanzu haka yanke wutar lantarki da ruwa da aka yi daga yankin ya shafi duk wanda ke zaune a Gaza. Mutane fiye d miliyan ɗaya ne ke buƙatar abinci, wannan ba labari ba ne mai kyau’’.
A ɓangare guda kuma rahotanni na cewa dakarun Isra’ila na ci gaba da matsawa kusa da Gaza, a wani ƙoƙari na aukawa ta ƙasa, bayan hare-haren sama.
Blinken na kan hanyar sauka a Isra'ila
Sakataren harkokin wajen Amurka tuni ya sauka a Isra'ila a wata ziyarar nuna goyon baya.
Bai je domin aikin shiga tsakani ba, wajen ganin an kawo ƙarshen wannan rikici: kuma bai yi kira a tsagaita wuta ba.
Sakonsa shi ne Isra'ila ta kwan da sanin cewa tana da goyon bayan Amurka - yau da gobe da kuma a ko yaushe.
Shi da Shugaba Biden sun tattauna a kan munin harin da Hamas ta kai: Sun ce dole Isra'ila ta ɗauki matakin kare kanta, kuma ta kawo ƙarshen wannan barazanar da take fuskanta, sannan ta tabbatar ta yi wa tufka hanci, ta yadda makamancin harin ranar Asabar ba zai sake faruwa ba nan gaba.
Sun nemi Isra'ila ta bi dokokin yaƙi na duniya, ta gujewa cutar da fararen hula, amma a bayyane take cewa suna so tare da goyon baya, ta yi amfani da dukkan ƙarfinta wajen murƙushe Hamas.
Amurkawan suna tattaunawa da Masar da kuma Isra'ila kan yadda fararen hula za su samu hanyar ficewa daga Gaza, amma lamarin cike yake da sarƙaƙiya in ji Blinken.
Adadin wadanda suka mutu ya karu
Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce mutum 1,200 ne suka mutu tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-harenta ta sama, a matsayin ramuwa kan harin da Hamas ta kai mata a safiyar ranar Asabar.
Mutuwar da aka samu a duka ɓangarorin biyu ta kusa kai wa 2,500.
Tun da fari, ma'aikatar harkokin tsaron Isra'ila ta ce an kashe Isra'ilawa 1,200 a harin Hamas na ƙarshen mako sai dai ana tsammanin adadin zai iya zarce haka.