Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Gaza ya ritsa da surukan shugaban gwamnatin Scotland
Shugaban gwamnatin Scotland ya ce surukansa sun maƙale a Gaza a daidai lokacin da ya yi kakkausar suka kan harin da Hamas ta kaddamar a Isra'ila.
Humza Yousaf ya ce mahaifan matarsa, wadanda suke rayuwa a Dundee, sun je Gaza ne duba kakar matarsa da ke kwance ba ta da lafiya.
Ƴan Isra'ila sun ce su fice daga yankin, sai dai Mista Yousaf ya shaida masu cewa babu wata hanya da za su iya amfani da ita su fice ba tare da wani abu ya same su ba, haka kuma ofishin jakadancin Birtaniya ba zai iya samar masu da mafita ba.
Ya ce shi da matarsa sun shiga damuwa sosai saboda tunanin ba za su tsira ba.
Mahaifan Nadia El-Nakla sun tafi Gaza ne mako guda da ya gabata suna kuma can Hamas ta kaddamar da hare-haren ban mamaki a Isra'ila, lamarin da ya kashe ɗaruruwan mutane.
Mista Yousaf ya shaida wa BBC cewa ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin na Hamas.
"Babu wata kumbiya-kumbiya game da yin Allah-wadai a kan haka, kuma gwamnatin Scotland ta yi amfani da kalamai masu kaushi wajen yin tur da hare-haren," in ji shi.
"Abin da muke iya gani shi ne mutanen da ba su ji ba su gani ba sun rasa rayuwarsu sakamakon hare-haren da aka kwashe sa'o'i 48 zuwa 72 ana yi.
"A wajena rayuwar ƴan isra'ilan da ba su ji ba su gani ba, daidai take da rayuwar Falasɗinawan da ba su ji ba su gani ba."
"Mutanen da babu ruwansu a kowane ɓangare suna rasa rayuwarsu, babu kuma wani dalili."
Shugaban gwamnatin Scotland ɗin ya ce "yahudawa mazauna Scotland sun shiga damuwa matuƙa kan iyalansu da ba su ji daga gare su ba."
Hukumomin Birtaniya sun shaida wa BBC cewa, sama da ƴan Birtaniya 10 ne suka mutu ko suka ɓace a Isra'ila bayan ƙaddamar da harin Hamas a isra'ilar.
An ga hoton Bernard Cowan ɗan birnin Glasgow a shafukan sada zumunta a lokacin da aka kashe shi yayin harin.
Mista Yousaf ya ce surukansa, Maged da Elizabeth El-Nakla sun je duba kakar matarsa ne, mai shekaru 92 a duniya, wadda ke fama da rashin lafiya a lokacin da Hamas suka kaddamar da harin.
Ya ce hukumomin Isra'ila sun shaida masu cewa su bar yankin Gaza "saboda za su shafe Gaza gaba ɗaya."
Gaza gari ne da ke dauke da mutane kusan miliyan 2.3, wadanda kashi 80 cikin ɗari sun dogara ne da ayyukan jin ƙai.
Sama da mutane ɗari 500 ne suka mutu a harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kaddamar, lamarin da ya haifar da koma baya ga ayyukan jin ƙai da ake gudanarwa a Gaza.
Mista Yousaf ya ce " Duk da ƙoƙarin da ofishin jakadanci Birtaniya ke yi, babu wanda zai iya bada tabbacin samar da hanyar da za su baro yankin cikin aminci."
"Ina cikin yanayi na fargabar ko Surukaina, wadanda ba su ji ba su gani ba, kamar yadda sauran ƴan Gaza da ba su da wata alaƙa da Hamas ko wani harin ta'addanci, ko za su tsira da rayuwarsu."
Ƙarancin abinci da ruwa
Tun bayan fara rikicin a ranar Asabar, Isra'ila sun dakatar da duk wani shige-da fice, wanda ya haɗa da kayan abinci da magani.
Mutane da dama na rayuwa babu wutar lantarki da intanet, kuma nan ba da jimawa ba za su rasa abinci da ruwan sha.
Tun a baya mazauna Gaza na fama da ƙarancin abinci da ruwa da kuma dokar hana zirga-zirga.
Ɗan uwan matar mista Yousaf na rayuwa a Gaza da yaransa huɗu ciki har da jariri ɗan wata biyu.
Mista Yousaf ya ce iyalan yanzu haka suna fuskantar ƙarancin madarar jarirai kuma kwana biyu kaɗai ya rage ma iyalan na a kai masu madarar.
Mista Yousaf ya sake jaddada cewa iyalansa ba su da wata alaƙa da Hamas.
Ya ce "Surukata malamar jinya ce da ta ajiye aiki a asibitin Ninewells, ɗan'uwana matarsa likita ce a Gaza, amman za su fuskanci hukunci tare da sauran yan Gaza, wanda kuma ba za a iya kare manufar yin hakan ba."
Shugaban ya ce yana magana da ofishin jakadanci.
"Zan iya yin duk mai yiyuwa domin bayar da goyon baya ga al'umar Yahudawa da Musulmai, wadanda suke cikin fargaba da tashin hankali, kuma zan tabbatar da na samar da kariya ga mutanen Scotland."
An tambayi Mista Yousaf ko ya kira mayakan Hamas da "ƴan ta'adda", sai ya ce "sosai kuwa, da babbar murya ma.
Shugaban ya ce hanya guda da za a iya samar da zaman lafiya a Isra'ila da Falasdinu ita ce maslahar kafa gwamnatoci biyu, ya ce kuma ƙasarsa ba za ta ɗaga tutar dukkan ƙasashen ba, illa kawai zai mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron ƴan Scotland da ke Isra'ila da Gaza.