Fenerbahce ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da Ozil

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fenerbahce ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da Mesut Ozil, duk da saura kaka biyu wa'adinta ya karkare.

Mai shekara 33 ya koma Fenerbahce a Janairun 2021, bayan da kwantiraginsa ya kare a Gunners, wanda yarjejeniyarsa ya kamata ta kare a karshen kakar 2024 da kungiyar Turkiya.

Rabon da Ozil ya buga tamaula tun cikin watan Maris, bayan da Fenerbahce ta dai na saka shi a wasanni.

Ana sa ran tsohon dan kwallon Arsenal da Real Madrid zai koma taka leda a Istanbul Basaksehir.

Ozil ya yi wasa 37 a dukkan fafatawa a kaka daya da rabi a Fenerbahce, da cin kwallo tara.