Me ya faru da Falasɗinawa 13,000 da suka ɓata a Zirin Gaza?

    • Marubuci, Amira Mhadhbi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • An wallafa

Yayin da adadin mutanen da ake kashewa a Zirin Gaza ke ƙaruwa, an yi ƙiyasin cewa sama da mutum 13,000 ne suka ɓata, kawai aka neme su aka rasa.

Ana kyautata zaton akwai da yawansu a ƙarƙashin ɓaraguzai, amma kuma masu fafautikar kare haƙƙi na zargin "ɓatar da wasu aka yi".

Ahmed Abu Duke ya shafe watanni yana neman ɗan'uwansa Mustafa.

Danginsa sun nemi mafaka a farfajiyar Asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Yunis bayan yaƙi ya raba su da gidansu. Sai dai kuma lokacin da suka ji labarin gidan da ke kusa da su ya harƙe da wuta sai Mustafa ya tafi ganin abin da ya faru. Tun daga loƙacin bai dawo ba.

"Mun duba iya iyawarmu," in ji Ahmed, yana mai cewa da akwai gidaje a wurin amma yanzu sai dai toka kawai da ɓaraguzai.

'Yan'uwansa sun yi ta neman Mustafa, wani tsohon direban motar marasa lafiya, a cikin gawar mutanen da hukumar ba da agaji ta Hamas ta gano ƙarƙashin ɓaraguzai da kuma katafaren ƙaburbura, amma ba su gan shi ba.

"Har yanzu muna fatan wata rana mu gan shi cikin wata motar gawa da za ta shigo asibiti," a cewar Ahmed.

Ma'aikatar lafiyar Gaza ƙarƙashin ikon Hamas ta ce Falasɗinawan da aka kashe a rikicin sun zarta 35,000, amma wannan adadi ya ƙunshi mutanen da aka kai asibiti ne kawai.

Akwai dangi da dama, kamar na Mustafa, da ba su san abin da ya faru da 'yan'uwansu ba cikin wata bakwai da suka wuce.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne Hamas da wasu mayaƙa suka tsallaka Isra'ila, inda suka kashe aƙalla mutum 1,200 tare da kama kusan 252. Isra'ila ta mayar da martani da kai hare-hare a kan Gaza.

Wata ƙungiyar kare haƙƙi a birnin Geneva mai suna Euro-Med Human Rights Monitor ta yi ƙiyasin akwai sama da 13,000 da suka ɓace. Sai dai alƙaluman ba su bambance tsakanin farar hula da mayaƙan Hamas ba.

Hukumar kare fararen hula da ake kira Civil Defence, wadda wani ɓangare ne na Hukumar Falasɗinawa, ta yi ƙiyasin akwai sama da mutum 10,000 da ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzai.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce yawan ɓaraguzan da ke Gaza ya kai tan miliyan 37 - inda gawarwaki suke jibge da kuma bamabamai masu nauyin tan 7,500 da ba su fashe ba, abin da ke ƙara zama barazana ga ma'aikatan agaji.

Civil Defence ta ce tana aiki tare da 'yan sa-kai don zaƙulo mutane amma kuma ba su da isassun kayan aiki da za su ba su damar kaiwa ga mutanen.

Haka nan akwai fargabar idan aka bar gawarwakin za su ruɓe, sannan kuma yanayin zafi ne ke tunkarowa a Gaza, wanda hakan zai iya zama haɗari ga lafiyar mutane.

Abdul Rahman Yaghi, shi ma ya fuskanci matsalar zaƙulo mmutane daga ɓaraguzai.

An kai wa gidansu hari da makami mai linzami ranar 22 ga watan Fabrairu daidai lokacin da 'yan'uwansa ke ciki a birnin Deir Al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

Ya ce an gano gawar mutum 17, amma kuma sassan jikin da aka gano ba za a iya tantance su ba.

"Ba mu gano akasarin gawar yaran da ke cikin gidan ba," in ji shi.

Civil Defence ta nemi agaji daga ƙasashen da ke da ƙwarewa da kuma MDD su taimaka wajen zaƙulo mutanen. Sai dai ta ce har yanzu ba ta samu amsa ba.

Ƙungiyar Amnesty International na ganin sauran mutanen da suka ɓace akwai yiwuwar dakarun sojin Isra'ila ne suka tsare su ba tare da sanin 'yan'uwansu ba, abin da suka fassara da "ɓatar da mutum".

Ƙungiyar Euro-Med Human Rights Monitor ta ce akwai ɗaruruwan Falsɗinawa da sojoji ke riƙe da su ba tare da an faɗa wa iyalansu ba. Yarjejeniyar Geneva - wadda Isra'ila ta saka wa hannu, ta sharɗanta cewa duk wata ƙasa da ta tsare farar hula wajibi ne ta faɗa wa iyalansa inda yake.

Haka nan, Isra'ila ta soke kai wa fursunoni Falasɗinawa ziyara da ƙungiyar Red Crescent (ICRC) ke yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Hisham Muhanna da ke aiki da ICRC a Gaza ya ce "sun sha neman a ba su damar ganawa da fursunoni Falasɗinawa...amma har yanzu ba a ba su dama ba".

Ta ƙara da cewa ba a ba ta damar kai wa Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su ba su ma.

BBC ta tuntuɓi sojin Isra'ila amma ba su ce komai ba.

Amma cikin wani saƙo da ya wallafa dandalin X, da aka sani da Twitter a baya, ministan tsaro na Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya ce: "Bai kamata Red Cross ta samu wasu bayanai game da fursunonin Falasɗinawa ba indai ba za a bari ta ga mutanen da ake garkuwa da su a Gaza ba: sai an ba mu za mu bayar!"

A garin al-Zawaid na tsakiyar Gaza, wani dangin na neman ɗansu. Suna fargbar yana cikin waɗanda aka tilasta wa ɓacewa.

Riƙe da hotonsa, mahaifiyar Mohamed Ali ta yi neman sa har sai da wani ya faɗa mata cewa sojin Isra'ila ne suka kama shi. Sun ce da ran sa lokaci na ƙarshe da suka gan shi, amma ba su san me ya faru ba bayan haka.

Mohamed ya ɓata tun ranar 23 ga watan Disamba lokacin da suka bar gidansu don samun mafaka a wata makaranta a Jabalia da ke arewacin Gaza sakamakon hare-hare.

Sojojin Isra'ila sun shiga makarantar kuma suka umarci mata da ƙananan yara su fice, a cewar matar Mohamed mai suna Amani Ali.

Ta ce dukkan mazan sun koma wajen 'yan'uwansu a wannan daren amma ban da Mohamed.

Har yanzu ba a san abin da ya faru da shi ba da kuma inda yake.

"Da yana raye zai neme mu kuma ya tarar da mu," kamar yadda Amani ta bayyana.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ƙirƙiri wani fam kuma ta umarci duk iyalan da suke da wani mutum da ya ɓata da su cika shi ta intanet don ta samu bayanan mutanen da suka ɓata tun daga 7 ga watan Oktoba.

Kafin lokacin, iyalai za su ci gaba da neman 'yan'uwansu da suka ɓata.