Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tawagar Spain ta mata ta zama ta ɗaya a jerin ƙasashen da Fifa ta fitar
Karon farko, Spain ta mata ta zama ta ɗaya a jerin tawagogi da Fifa ke fitar da jadawalinsu, yayin da Ingila ta kasance a matsayi na huɗu.
Spain ce ta cinye Ingila 1-0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya ta mata da aka yi a watan Agusta, ta zama ƙasa ta huɗu, da ta taɓa rike irin wannan matsayi a tarihi.
Waɗanda ke riƙe da kambun a baya, Sweden sun faɗi zuwa matsayi na biyar, yayin da Amurka da ta taɓa zama ta ɗaya, a bana ta koma ta biyu, Faransa kuma ta koma ta uku daga ta biyu.
Scotland ta koma ta 25 ita kuwa Wales na matsayi na 32, yayin da Northern Ireland ke ta 46.
Jamus da Netherland da Japan na riƙe da matsayinsu na baya ta shida, da ta bakwai da ta takwas baki ɗaya, Koriya ta Arewa na matsayi na tara sai kuma Canada da take ta 10.
Brazil da ta gaza fitowa daga matakin rukuni a Kofin Duniya a wannan shekara karon farko tun 1995, ta fita daga jerin ƙasashe 10 a jadawalin na Fifa, yanzu tana matsayi na 11.
Cikin jerin ƙasashe 30 na farko-farko a jadawalin, babu ko ɗaya daga nahiyar Afrika, don kuwa Najeriya ta ɗaya a Afirka, tana matsayi na 34 a jadawalin ƙasashen duniya.