Chelsea ta fara da 1-1 karkashin sabon koci Potter

Champiobs League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Graham Potter ya fara da jan ragamar Chelsea da yin 1-1 da RB Leipzig a Stamford Bridge a wasa na biyu a Champions League ranar Laraba.

A wasan na farko da ya fara a gida ya sa Raheem Sterling ya buga karawar daga gefe, hakan ya sa dan kwallon Ingila ya ci Salzburg.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta taka rawar gani fiye da wadda ta yi rashin nasara a Dinamo Zagreb 1-0 a wasan farko karkashin Thomas Tuchel.

To sai dai kuma Matthias Jaissle ne ya farke kwallo, saura minti 15 su tashi daga wasan.

Daga baya mai masaukin baki ta kusan kara na biyu, bayan da Reece James ya buga kwallo a bugun tazara, inda Hakim Ziyech ya kusan taba ta da kai ta fada raga.

Daya wasan na rukunin AC Milan ta ci Zagreb 3-1, hakan na nufin Chelsea tana ta karshe a rukunin, bayan buga karawa biyu.

Chelsea za ta karbi bakuncin kungiyar Italiya a wasa na uku a cikin rukuni a babbar Gasar Zakarun Turai ranar 5 ga watan Oktoba.

Champiobs League

Asalin hoton, BBC Sport