Labaran matan Afirka ta Kudu takwas da aka yi wa fyaɗen taron dangi

Outraged citizens and political parties alike have decried the attack

Asalin hoton, SHIRAAZ MOHAMED

Bayanan hoto, Ƴan Afirka ta Kudu sun yi zanga-zanga kan wannan fyaɗen taron dangin
An wallafa

Wasu na cewa a sanya dokar ta ɓaci a Afirka ta Kudu, bayan da fyaɗen taron dangi da aka yi wa wasu mata takwas a lokacin da suke naɗar bidiyon rawa a watan da ya wuce.

Lamarin ya faru ne a wani wajen haƙar ma'adinai da aka daina amfani da shi a garin Krugersdorp.

Sai dai har yanzu ba a gurfanar da kowa daga cikin mutum 130 da ake zargi da hannu a lamarin ba, saboda ƴan sanda sun ce suna jiran sakamakon gwajin ƙwayoyin halitta da aka ɗauka tukunna.

Yawancin wadanda ake zargin masu haƙar ma'adinai ne ba tare da izini ba a wajen da aka daina amfani da shi ɗin.

Mafi yawansu ƴan ci rani ne daga ƙasashe maƙwabta, abin da ya sa wani cincirindon mutane suka fara kai wa baƙi masu haƙar ma'adinai hari a gidajensu a matsayin ramuwa.

Uku daga cikin matan da aka yi wa fyaɗen sun bayyana gumurzun da suka sha, wanda ya sa suka shiga ruɗani da fita hayyaci.

Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da tashin hankali na cin zarafin mata

"Mun zata mutuwa za mu yi," in ji ɗaya daga cikin waɗanda aka yi wa fyaɗen.

"Kawai gani muka yi sun ɓullo daga cikin jeji da ramukan haƙa suna harba bindigogi, suna ce mana mu kwanta a ƙasa.

"Wasun mu sun so su gudu amma sai suka kamo su.

"Abin da ya biyo baya wani abin tsoro ne da tayar da hankali na awannin da aka ɗauka ana yi mana fyaɗe.

"Kawai muna kwance mun sadaƙat mun rirriƙe hannayen juna... Na zaci mutuwa zan yi, zan mutu hannuna maƙale da na ƴar uwata... Sai muka yi ta addu'a kawai.

An ware ɗaya daga cikin matan saboda ƙirar jikinta.

"Suka ce min ni ramammiya ce ba ni da mamora.

"Kawai sai suka jefa ni a cikin wani rami suka so binne ni da raina," in ji ta.

Three of the gang rape survivors have spoken anonymously

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Mata uku daga cikin wadanda aka yi wa fyaɗen sun ba da labarin abin da ya same su
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ita ma wata daga cikin wadanda aka yi wa fyaɗen, ta ba da labari cikin shessheƙar kuka, inda ta ce an mata duka saboda ta ƙi bayar da haɗin kai cikin sauƙi.

"Ya tunkuɗe ni ya ce min na sa kayana, amma sai sauran suka dinga bi ɗaya bayan ɗaya suna amfani da ni a yayin da ɗaya yake tsaye a kaina riƙe da bindiga.

"A wannan lokacin ne na sadaƙat. Na zaci mutuwa zan yi. Ba ni da ƙarfin yin faɗa da su, kuma ba zan iya tsira ba," ta faɗa.

"Na zaci mutuwa zan yi kamar yadda mata da yawa suka sha mutuwa sakamakon fyaɗen da aka yi musu a ƙasar nan.

Matan da aka yi wa fyaɗen a garin Krugersdorp suna kira ga ƴan sanda da su yi duk mai yiwuwa don gurfanar da waɗanda suka aikata musu hakan.

"So muke su dauwama a gidan yari, muna so a dinga ba mu kariya dare da rana ta yadda ba za mu dinga jin tsoron zuwa ko ina ba duk lokacin da muke so.

"Muna so mu taimaka wa ƴan sanda wajen binciken da suke yi ta yadda za a yi saurin gane mutanen a kuma gurfanar da su a gaban kotu.

"Za mu yi hakan ne saboda bin hakkin sauran matan da aka sha kashewa ta wannan hanya a baya."

Ɗaukar doka a hannu

Mutanen garin da lamarin ya faru sun harzuƙa suna neman ƴan sanda su ɗauki tsauraran matakai, inda suka yi zanga-zanga a garuruwa da yawa da ke kusa da wajen haƙar ma'adinan da ke yamma da birnin Johannesburg.

Wasu daga cikinsu sun yi wa waɗanda ake zargi da haƙar ma'adinai tumɓur tare da zane su, sun kuma ƙona gidajensu, a ƙoƙarin ɗaukar doka a hannu.

Sun zargin ƙungiyoyin masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba na Zama Zama da cewa su ne ke da hannu a manyan laifuka da ta da zaune tsaye da fyaɗen taron dangin da aka yi wa mata takwas, ƴan tsakanin shekaru daga 19 zuwa 35.

"Babu wanda ya tsira a nan idan dai har ƙungiyar Zama Zama tana nan - shi ya sa gara mu ɗauki doka a hannunmu," in ji wani mai zanga-zanga.

Ana ci gaba da samun ƙaruwar kai wa baƙi hare-hare a Afirka ta Kudu a shekarun bayan nan.

Arsonists targeted the homes of suspected foreign miners

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Mutane sun kai wa masu haƙar ma'dinai hari a gidajensu

Sai dai akwai mazauna garin da suka shiga sahun masu zanga-zangar da ke fargabar kai a kai musu harin ramuwa.

Ƴan sanda dai sun sha alwashin kare mata, bayan da mutane suka zarge su da cewa ba sa yin yadda ya kamata.

Ministan ƴan sanda na ƙasar Bheki Cele a lokacin da yake yi wa mutane jawabi, ya ce "Fyaɗe ya yi yawa a nan, mutane sun mayar da shi kamar wani abin kirki."

Ya ce ba za su bari irin hakan ta ci gaba da faruwa a ƙasar ba.

Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen duniya da ke fama da matsalar fyaɗe, kuma ba a faye yanke wa masu yi hukunci ba.

A yanzu, mafi yawan ƴan ƙasar na tababar ko za a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata wannan fyaɗe na taron dangi a kuma yanke musu hukunci.

Yayin da wasu kuma ke tsoron cewa masu aikata laifin za su ci gaba da cin karensu babu babbaka ne suna rusa rayuwar mutane.