An gurfanar da mutumin da ake zargi da yi wa 'yar shekara hudu fyade a kotu a Kano

Asalin hoton, Getty Images
An gurfanar da wani mutum a gaban wata kotun majistare a ke jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya bisa zargin yi wa wata yarinya yar shekara hudu fyade, abin da kuma yayi sanadiyyar mutuwarta.
Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa fyaden da aka yi mata ne yayi sanadin mutuwarta.
Sai dai har yanzu ana jiran rahoton likita da zai yi bayani kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Yayin da aka gurfanar da mutumin mai shekara arba’in a gaban kotun, lauyoyin gwamnati masu gabatar da kara sun shigar da tuhuma daya, inda aka karanto masa cewa ana zarginsa da yi wa yarinyar ‘yar shekara hudu fyade cikin watan jiya a unguwar Kwana hudu cikin karamar hukumar Nasarawa.
Barista Bello Isa Lawan shi ne lauyan gwamnati da ya jagoranci gabatar da wannan tuhuma, ya kuma shaida wa BBC cewa ''An kawo shi kotu, an kuma karanta masa abinda ake tuhumarsa da shi , wanda shi kuma ya musa wannan tuhuma da ake yi masa, to shi ne muka gaya wa kotu cewa muna so a ba mu watarana, domin abinda ake zarginsa da shi , abu ne mai girma wanda ita wannan kotun ba ta da hurumin sauraron wannan shari'a, to mun karbi kundin tuhumar kuma za mu kai wa babban jami'in shigar da kara, zai zauna ya yi nazari domin ganin abin da ya kamata a yi, domin yi wa kowanne bangare adalci.''
Barista Bilya Abubakar Muhammad dan uwan yarinyar da ta rasu ne kuma lauyan da ke bin diddigin wannan shari’a, ya ce suna fatan kafin zaman kotu na gaba za a samu bayani kan abin da ya yi sanadin mutuwar yarinyar. Ya kuma shaida wa BBC cewa ''Mun yi magana da 'yan sandan da ke bincike, sun fada mana cewa sun rubuta wa asibiti domin samun rahoton musabbabin mutuwar yarinyar, shi ne yasa ba su hada rahoton tuhumar kisan kai ba, amma suna jiran rahoto daga asibiti, da zarar sun samu, za su kawo domin tuhumarsa da abin da ya dace'', Akaliyar kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, ta kuma dage wannan shari'ar zuwa ranar bakwai ga watan gobe. Matsalar fyade ta jima tana ci wa al'uma tuwo a kwarya a Najeriya, kuma al’amarin bai tsaya a kan manya ko 'yan mata kadai ba, har da kananan yara da jarirai. A ko da yaushe ana shawartar mazauna unguwanni musamman iyaye da su kara sanya ido a kan take-take da kai-komon mutane a yankunansu, da nufin kare 'ya'yansu da kuma iyalansu daga masu aikata fyade.







