Yadda kuɗin sulalla ya zame wa wasu ma’aurata alaƙaƙai

An wallafa

Wasu ma’aurata sun shiga cikin yanayi mara dadi sakamakon wasu tsabar kudi da suka gani a cikin ginin karkashin ƙasa na gidan da suke zaune.

Ma'auratan sun yi hasashen kudin sun kai miliyoyi masu yawa.

John Reyes da matarsa sun ga jakar kudaden ne lokacin da suke wanke gidan mahaifinta da ya rasu a birnin Los Angeles kimanin watanni tara baya.

Ma’auratan sun yi shirin rika amfani da kudin amma daga baya suka rike su.

Wani banki ya shaida wa Ryes cewa ba su da kurin da za su ajiye waɗannan tsabobin.

“Ka da ka kawo su nan,” in ji Manajan reshen bankin Well Fargo, kamar yadda ya bayyana a wata tattaunawa da ya yi da CBS.

Sun gano kudin ne lokacin da ya tsoguna kan bwiwowinsa yana bincike cikin ma’ajiyar sirikin nasa a gidansa da ke Pico-Union mai makwabtaka da Loss Angeles.

Da farko cewa ya yi sun tsinci wasu karfuna masu daraja da aka rufe da takardu. Amma daga baya sai suka gano jakankunan banki ne ɗauke da tsabar kuɗaɗen.

“Wasu bankunan da suka ga jakankunansu yanzu ba ma sa aiki baki daya,” in ji Reyes.

“Sai da muka ɗauki jaka ɗaya bayan ɗaya muka fitar da su daga gidan kasan, muka hau sama, muka shigar da su mota ta,” Mista Reyes ya ci gaba da cewa sai da suka ɗauki kwana guda suna kwashe kuɗaɗen.

An gida gidan da suke ne a farkon shekarun 1900 kuma iyalan sun yi amannar cewa wurin hutu ne da tattaunawa a gare su.

Sulallan waɗanda aka yi da tagulla, an yi shi ne tun 1943, lokacin da Amurka ta yi amfani da wasu ƙarafa domin yin santi daya saboda ƙarancin ƙarafan bayan yaƙin duniya na biyu. Amma yanzu da ƙarfen da ake kwanon langa-langa ake yin sulalla a Amurka.

Nauyin sulallan sai da suka durƙusar da motarsu abin da ya sanya suka koma yankin masu tafi a hankali kenan a kan titi, in ji ma’auratan.

Ba su ƙirga kuɗin ba buhu bayan buhu, amma a hasashensu kuɗaɗem sun haura miliyan.

Bayan tattaunawa da wani ma’aikacin banki, cikin ɓacin rai ma’auratan suka sauya tunanin canja kuɗin.

“Ka ga irin labaran nan ba su dadin ji na ke cewa mutane sun samu kuɗin da suka kai dala miliyan 2,” in ji Reyes.

Mai makon cin buri kan kuɗaɗen, daga ƙarshe sun yanke shawara kan su sayar da su a intanet ko dala 25,000 su samu.

Reyes ya ce kudaɗen za su taimaka musu wajen gyara gidan sai a bayar da shi haya ga wasu.

Ya ce kuɗin sai da suka sa shi ya riƙa jin duk da surukinsa ya rasu, amma ya bar wani abu mai kauri da zai sa su riƙa tunawa da shi.