PSG na tattaunawa da wakilin Rashford, Madrid za ta dauko Bravo

Asalin hoton, Reuters
Paris St-Germain na tattaunawa da wakilin Marcus Rashford game da yiwuwar daukar dan wasan gaban na Ingila, mai shekara 24, wanda ke buga wasa a Manchester United. (L'Equipe - in French)
United a nata bangaren ta shirya tattaunawa da mahaifiyar Adrien Rabiot da wakilinsa, bayan daidatawar da kungiyar ta yi da Juventus kan farashin dan wasan na tsakiya dan asalin Faransa, mai shekara 27. (Fabrizio Romano)
Manchester City kuwa ta nuna sha’awar sayen dan wasan baya na Atletico Madrid, dan asalin kasar Brazil, Renan Lodi, mai shekara 24. (Telegraph - subscription required)
Shi ma dan wasan baya na Scotland da ke wasa a Arsenal, Kieran Tierney, mai shekara 25, na daga cikin sunayen ‘yan wasan da Manchester City ke kyallara idonta a kansu. (90min)
Tsohon dan wasan gaba na Arsenal, dan asalin Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33, zai fi son ya ci gaba da taka leda a Barcelona, a maimakon komawa Chelsea domin buga gasar Premier ta Ingila. (Sport, via Metro)
Nottingham Forest ta fara taya dan wasan gaba na Watford, dan asalin Najeriya Emmanuel Dennis, mai shekara 24. (The Athletic)
Atalanta za ta fafata da Forest a kokarin sayo dan wasan baya na gefen hagu dan asalin kasar Italiya Emerson Palmieri, mai shekara 28, daga Chelsea. (Standard)
Dan wasan Southampton, Che Adams na son tafiya Everton, sai dai kungiyoyin Leeds United, da Wolves da kuma Forest su ma suna son ganin sun dauki dan wasan gaban na Scotland, mai shekara 26. (Mail)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Everton na sa ran kammala yarjejeniyar daukar dan wasan gaba na kasar Guinea, Serhou Guirassy, mai shekara 26, daga Rennes kafin karshen wannan mako. (L'Equipe - in French)
Tsohon mai rikon mukamin kociyan Manchester United, Ralf Rangnick ya bai wa dan wasan gaba na Stuttgart, dan asalin kasar Austria, Sasa Kalajdzic, mai shekara 25, shawarar kin amincewa da tayin komawa buga wasa a Old Trafford. (Star)
West Ham na ci gaba da tattaunawa da Paris St-Germain a kan kokarinta na sayo dan wasan baya na Jamus, Thilo Kehrer, mai shekara 25. (Express)
Roma ta sassauta kan yunkurinta na sayar da Nicolo Zaniolo, mai shekara 23, dan asalin kasar Italiya, wanda ake alakantawa da Tottenham. (Standard)
Everton na yunkurin sayen sabon dan wasa na hudu a cikin mako guda, inda tattaunawa ke tafiya yadda ya kamata a kokarinta na sayo Ludovic Ajorgue, mai shekara 28, dan asalin Faransa, daga kungiyar Strasbourg. (Foot Mercato, via Express)
Juventus na gab da cimma yarjejeniya da Barcelona domin dauko dan wasan gaba na Netherlands, Memphis Depay, mai shekara 28. (90min)
Marseille ta tuntubi Manchester United kan yukurinta na daukar dan wasan baya na Ivory Coast mai taka leda a Old Trafford, Eric Bailly, mai shekara 28, a matsayin aro. (L'Equipe - in French)
Dan wasan gaba na Sifaniya da Bayer Leverkusen, Iker Bravo, mai shekara 17, zai tafi Real Madrid a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda. (Bild - in German)
Kungiyar Watford, da Burnley, da Blackburn Rovers da kuma Sheffield United, wadanda ke wasa a mataki na biyu (Championship) a kasar Ingila na takarar daukar dan wasan baya na Netherlands da Liverpool, Sepp van den Berg, mai shekara 20, a matsayin aro. (Mail)
Tsohon dan wasan gaba na Sifaniya da Chelsea, Diego Costa, mai shekara 33, zai koma Rayo Vallecano, bayan gaza samun kungiya tun bayan da kwantaraginsa ta kare da Atletico Mineiro a watan Janairu. (Marca)











