Morocco ta kori kocin da ya sama mata gurbin Kofin Duniya

Vahid Halilhodzic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vahid Halilhodzic ya taimaka wa Ivory Coast da Japan da Morocco samun gurbin gasar Kofin Duniya amma duka suka kore shi kafin a je
An wallafa

Moroko ta sallami mai horad da 'yan wasanta Vahid Halilhodzic wata uku kafin gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce an dauki matakin raba gari da kociyan ne sakamakon rashin jituwa kan yadda za a shirya tawagar kwallon 'yan wasan kasar Atlas Lions yadda za ta je gasar ta duniya.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an rabu ne cikin ruwan sanyi, ba dutse hannun riga ba.

Tun a watan Agusta na 2019 Halilhodzic, mai shekara 69, ya karbi aikin horad da tawagar 'yan wasan kasar da ke Afirka ta Arewa.

Kociyan dan kasar Bosnia ya kai kasar zuwa wasan dab da na kusa da karshe (wato quarter-finals) a gasar cin Kofin Kasashen Afirka a Kamaru.

Sannan kuma ya samar wa kasar gurbi a gasar cin Kofin Duniya bayan nasara a kan Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo da ci 5-2, jumulla wasa gida da waje.

Yanzu dai ana ganin tafiyar kociyan ta share hanyar komawar dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech tawagar kasar ta Moroko, saboda 'yar tsamar da ke tsakaninsu, kasancewar shugaban hukumar kwallon kasar Fouzi Lekjaa ya ce kofa a bude da ke ga dan wasan ya koma.

Daman tuni ake rade-radi game da makomar kociyan saboda an ruwaito Lekjaa na cewa dan wasan na Chelsea zai kasance cikin tawagar da za ta je gasar Kofin Duniya.

Moroko za ta kara da Crotia da Belgium da kuma Kanada a rukuni na 6 wato Group F a gasar ta duniya.

Wannan shi ne karo na uku da wata kasa da kociyan ya sama wa gurbin gasar Kofin Duniya ke sallamarsa kafin a tafi wasan.

A baya Halilhodzic ya sama wa Ivory Coast da Japan tikitin zuwa cin Kofin Duniya, amma kuma kasashen suka sallame shi kafin tafiya gasar.