Chelsea ta dauki Maresca sabon mai horar da ita

An wallafa

Chelsea ta sanar da ɗaukar Enzo Maresca a matakin sabon kociyanta, domin jan ragamar ƙungiyar Stamfor Bridge daga 2024/25.

Mai shekara 44 zai horar da tamaula a Premier League daga badi, bayan da ya kai Leicester City babbar gasar tamaula ta Ingila daga Championship.

Maresca, wanda yanzu zai koma aiki da ƙungiyar Stamford Bridge ya mayar da Leicester City Premier League kaka daya kacal da ya ja ragama.

Maresca ya maye gurbin Mouricio Pochettino, wanda ya yi aikin kaka daya tare da Chelsea.

Ƙungiyar Stamford Bridge ta kare a mataki na shida a teburin Premier League da aka kammala, za kuma ta buga wasan cike gurbin Europa Conference League.

Maresca kociyan Chelsea na hudu cikin shekara biyu

Kamfanin hannun jari karkashin Todd Boehly ne ya mallaki Chelsea a 2022.

A lokacin Thomas Tuchel ne ke jan ragama, wanda ya ci wasa biyu a Champions League tare da Chelsea.

To sai dai ƙungiyar ta fara kakar da aka kammala da mugun zare, kuma hakan ya sa aka kori ɗan kasar Jamus, kuma an yi ta takaddama kan dalilin da aka kori Tuchel.

Graham Potter ne ya maye gurbin Tuchel, wanda aka sa ya bar Brighton, wadda ya bunkasa wasanninta.

Kociyan ya ja ragamar wasa 31, wanda aka doke shi karawa 11 da ta kai an sallame shi daga aikin a cikin Afirilun 2023, kasa da wata bakwai da aka bashi jan ragama.

Daga nan Chelsea ta nada Bruno Saltor da Frank Lampard a matakin riƙon ƙwarya, bayan korar Poter.

Ƙungiyar da ke Stamford Bridge ta dauki Mauricio Pochettino a cikin watan Mayun 2023, wanda suka raba gari bayan kammala kakar da aka kammala.

A karkashin kociyan ɗan kasar Argentina, Chelsea ta yi ta biyu a League Cup da Liverpool ta lashe da kai wa daf da karshe a FA Cup.

Ko mai ya sa Chelsea ta dauki Maresca

Chelsea ta zaɓ ɗaukar Enzo Maresca daga cikin wadanda ta tuntba, domin maye gurbin Mauricio Pochettino.

Tun farko ta tsara tuntubar kociya da suka hada da na Ipswich, Kieran McKenna da tsohon na Brighton, Roberto De Zerbi da kuma na Brentford, Thomas Frank.

An zaɓi ɗan kasar Italiya, mai shekara 44, wanda ya ƙware wajen hada ƙididdiga da ƙwazon ɗan wasa da hada kimiya a gudanar da aikin horar da tamaula

Ƙungiyar tana watsi da batun kociya ya ja ragamar ɗaukar ƴan wasa, an fi son ya mayar da hankali kan bunkasa ƙwallon kafar ƙngiya da ƴan wasan da yake da su a kasa.

Hakan ne ya sa aka samu matsala tsakanin mahukuntan ƙungiyar da Pochettino da ta kai dole ya hakura da jan ragamar Chelsea.

Maresca kuwa ya ƙware kan bunkasa ƙungiya tun daga matasanta da kuma tsara fuskantar ƙalubalen kowanne wasan da ke gabansa.

Tuni Maresca ya bukaci a bashi bayanan kowanne ƴan wasan ƙungiyar har da na matasa da jami'anta, tun kan ya fara aiki daga 1 ga watan Yuli.

Wannan tsarin ya faranta ran Chelsea kan yadda take fatan zai bunkasa ƙungiyar, wadda tuni take fatan ɗaukar Tosin Adarabioyo daga Fulham.

Ana sa ran Maresca zai gayyaci matasan ƙungiyar cikin Chelsea da suka hada da Tyrique George da kuma Josh Acheampong, bayan da ake sa rran fitattun ƴan wasan za su koma taka leda da zarar an kammala Euro 2024 da kuma Copa America.

Chelsea na fatan Maresca zai mayar da ƙungiyar kan turba, saboda irin fitattun ƴan wasan da take da su da kuma ƙwarewar da yake da ita, wanda aiki da ya yi tare da Pep Guradiola ake ganin yana turbar zama gwani a fannin horar da tamaula a duniya.