Me ya sa abincin Afirka bai fiye jan hankali ba a duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Wata fitacciyar mai dafa abinci a Zambia ta shaidawa BBC cewa ba ta daukin jadawalin da aka fitar kan nau'ikan abinci mafiya daɗi a duniya da muhimmanci ba.
Kalamanta na zuwa ne bayan shafin girke-girke na Taste Atlas, da ke bibbiyar nau'ikan abinci na duniya kama daga na gargajiya zuwa abinci Turawa da na 'yan Asiya da Afirka ya wallafa jeren abinci 95 da suka fi daɗi a duniya a 2022.
Ƙasashen Afirka Uku ne kaɗai suka kai labarin cikin jeren ƙasashe 50, ciki akwai Algeria da Afirka ta Kudu da kuma Tunisia.
Shafin Taste Atlas ya ce sun fitar da wannan jadawali ne bisa kuri'ar mutane kan sinadaran girki ko haɗa abinci da ɗandano, yanayin girki da kuma lemukan sha.
Ƙasashen Italiya da Girka da Sifaniya da Japan da Indiya suke sahun farko na ƙasashe biyar.
Sai dai ana ta samun masu ɗiga ayar tambaya kan wannan jadawali da kuma dalilan da suka sa ƙasashen Afirka kalilan ne cikin ƙasashe 50 da suka fito a jeren jadawalin.

Asalin hoton, Getty Images
Masu zuwa yawon bude ido ne suka kaɗa wannan kuri'a, a cewar Lillian Elidah, kwararriyar mai dafa abinci da kuma ke da kantin sayar da abinci na Twaala a birnin Lusaka.
Ƙasashen da suke cikin rukunni ƙasashe 10 a saman teburi, sun kasance ƙasashe da turawa ke yawaita zuwa yawon buɗe ido, don haka dole su zaɓe su, a cewarta.
Ms Elidah ta ce akwai bukatar masu girka abinci iri daban-daban a Zambia su inganta yada suke gabatar da abincinsu da kuma gabatar da shi ta yada zai rinƙa jan hankali.
Amma dai abu ne mai wahala 'yan Zambia su rungumi nau'ikan abincinsu na gargajiya, a cewarta.

Asalin hoton, Getty Images
"Galibin sinadaran ɗanɗano a girki da abincinmu sun rasa tushensu, wanda galibin mutane ke danganta hakan da talauci, don haka suna fama da talaucin jure sayen irin waɗannan abincin, don haka ba sa ci."
Ta ce ba ta yarda cewa dole sai ka ziyarci Zambia kafin ka samu damar ɗanɗana abincinsu ba.
"Ya kamata a ce akwai tsarin kwaɗaitawa duniya da jan hankali kan nau'ika ko ire-iren abincin Afirka.
Ana iya soma hakan ta hanyar bijiro da shirye-shirye, samun bayanai da kuma amfani da kofofin sada zumunta, wannan zai kasance hanya mai sauki."
Hukumomin da ke sa ido kan harkokin yawan buɗe ido a duniya su habbaka ayyukansu wajen ganin sun tallata ire-iren abinci Afirka masu jan hankali, a cewarta.
"Horar da masu girki da sayar da abinci" zai taimaka wajen ganin abinci Afirka ya isa ga ko ina a duniya, a cewarta












