Ian Maatsen: Dan wasan Chelsea zai yi wasannin aro a Borussia Dortmund

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Chelsea, Ian Maatsen ya amince zai buga wasannin aro a Borussia Dortmund zuwa ƙarshen kakar bana.
Mai shekara 21, zai fara saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa a Stamford Bridge, kafin ya je ƙungiyar da ke buga Bundesliga.
Cikin ƙunshin kwantiragin da zai je Jamus buga wasannin aro, babu batun sayar da dan kwwalllon ko da ya taka rawar gani a Dorrtmund din.
Sai dai Chelsea za ta iya sayar da ɗan wasan mai shekara 21 a ƙarshen kakar bana, bayan da ƙungiyar ke fatan bin dokar hukumar ƙwalllon ƙafar Turai ta kashe kuɗi daidai samu, bayan kashe kuɗi mai yawa da ta sayi ƴan ƙwallo da yawa.
Chelsea ta amince da tayin £31.5m daga Burnley kan fara kakar bana, amma Maatsen bai amince ya bar Stamford Bridge ba.
Ɗan kwallon tawagar Netherlands ta matasa ƴan ƙasa da shekara 21 ya buga wasa uku a bana, yayin da ya yi zaman benci karo 12.
Lokacin da ya buga wasannin aro a Burnley a kakar da ta wuce, Maatsen ya taka rawar gani da ƙungiyar ta lashe Championship yana cikin ƴan wasan da ƙungiyar ta so yin amfani da shi a Lik a bana.
Chelsea na fatan sayen mai cin ƙwallo a watan nan na Janairu, amma da ƙyar ne idan za ta samu Victor Osimhen daga Napoli ko ɗan ƙwallon Brentford, Ivan Toney.
Ƙungiyar da Mauricio Pochettino ke jan ragama za ta fuskanci Middlesbrough a Carabao Cup a daf da ƙarshen wasan farko ranar Talata.











