Waiwaye: Zaman sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano a kotun ƙoli da rage kuɗin mota ga matafiya
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin ƙarshe kan zaɓen gwamnan Kano

Kotun ƙoli ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin ƙarshe kan shari'ar gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC.
Kotun ta bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan zaman da ta yi na farko kan ƙarar da gwamna Abba Kabir ya shigar gabanta.
Gwamnan na jam'iyyar NNPP ya shigar da ƙarar domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
A zaman kotun na ranar Alhamis, Mai shari'a John Okoro, wanda shi ne jagoran alƙalan, ya buƙaci ɓangarorin da ke cikin shari'ar su samu matsaya kan ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafe tara da aka ɗaukaka ƙara a kai, wanda hukuncin da za a yanke kan sa zai shafi sauran ƙorafe-ƙorafen takwas.
Tinubu ya rage rabin kuɗin mota ga matafiya a Najeriya

Asalin hoton, TINUBU/FACEBOOK
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rage kuɗin sufuri ga ‘yan Najeriya da kashi 50 cikin 100.
Ministan ma’adanai na ƙasa, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai ranar Laraba kan tallafin shugaban ƙasa a harkokin sufurin jama’a domin murnar bikin Kirsimeti a Abuja.
Tallafin ya fara aiki tun ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, kuma zai ƙare a ranar 4 ga Janairun 2024.
"Ƴan Nijeriya masu son yin balaguro za su iya hawa motocin haya na kamfani a kan rangwamen kashi 50% na farashin da ake kashewa a halin yanzu, da kuma duk tafiyar da za a yi a kan hanyoyin jiragen ƙasa a halin yanzu ba tare da sun biya kuɗi ba a wannan lokaci na hutu.” in ji shi.
Ya yi bayanin cewa Shugaba Tinubu ya amince da hakan ne domin nuna soyayyarsa ga ‘yan Najeriya, inda ya ƙara da cewa matakin ya bai wa ‘yan Najeriya da ke son yin balaguro don ziyartar ‘yan uwansu da garuruwansu damar yin hakan ba tare da damuwa ba yayin da tsadar rayuwa ke ƙamari a wannan lokacin.
Alake ya bayyana cewa Tinubu ya umurci ‘yan sanda da hukumar DSS da sojoji da sauran jami’an tsaro su haɗa kai don ganin an gudanar da bukukuwan lafiya ba tare da taɓarɓarewar tsaro a kowane ɓangaren ƙasar ba.
Yadda aka sace sarki da fadawansa a Taraba

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Pupule na yankin karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba, inda suka sace mutum 23 ciki har da basarake mai daraja ta biyu da fadawansa.
Lamarin ya afku ne a ranar Talata da daddare inda ‘yan bindigar masu yawan gaske suka shiga garin tare da kewaye shi.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, ba su san adadin ‘yan bindigar da suka shiga garin nasu ba saboda yawansu.
Ya ce,” sun shiga cikin dare suka dauki na dauka suka bar na bari, kuma a cikin wadanda suka dauka baya ga basaraken da dogarinsa, akwai limamin masallacin Jumma’a da fastoci biyu da kuma sauran jama’ar gari.”
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun fasa shaguna tare da satar kayan abinci da abubuwan sha.
Ƴan majalisar Rivers sun janye ƙudirin tsige gwamna Fubara

Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT HOUSE MEDIA
Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers da suka koma jam'iyyar APC sun janye ƙudirinsu na son tsige gwamna Siminalayi Fubara.
Ƴan majalisar ƙarƙashin shugaban ɗaya ɓangaren Martin Amaewhule sun janye ƙudirin bayan sun koma zama a ranar Laraba.
Hakan ya faru ne sakamakon shiga tsakanin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi domin sasanta ɓangarorin biyu.
Sai dai kwamishinan yaɗa labarai, Joseph Johnson ya musanta masaniya kan hakan.
Ya faɗa wa jaridar Vanguard cewa gwamnatin jihar ba ta san da wannan batu ba.
Ƴan majalisar sun ce sun sauya matsayar ne domin mutunta yarjejeniyar da aka cimma domin sasanta rikicin.
A takardar sanar da janyewar da aka karanta a zauren majalisar, ƴan majalisar sun ce sun ɗauki matakin ne a matsayin girmamawa ga shugaban ƙasa.
An rantsar da Simon Lalong a matsayin sanata

Asalin hoton, @SIMONLALONG
An rantsar da tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, a matsayin ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Filato ta Kudu.
An rantsar da shi ne a lokacin zaman zauren majalisar na ranar Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan Lalong ya ajiye muƙaminsa na ministan ƙwadago a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata wasiƙa da ya gabatar wa shugaban ƙasa a ranar Talata, ministan ya tunatar da shugaban ƙasar cewa kotun ɗaukaƙa ƙara ta bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen sanata mai wakiltar Mazabar Filato ta Kudu tare da bayar da umarni ga hukumar zaɓe INEC ta miƙa masa shaidar nasarar cin zaɓe.
Lalong ya ce bai yanke shawarar murabus daga minista cikin hanzari ba saboda amanar da shugaban ƙasa ya damƙa masa a matsayin minista a majalisar zartarwa bayan ya rike mukamin darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC.
Za mu hukunta likitocin da ke safarar ƙoda a Najeriya – Gwamnati

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta bayar da tabbacin ɗaukan mataki kan likitoci da sauran mutanen da ke da hannu a harkar safarar ƙoda.
Jami'ar yaɗa labarai ta ma'aikatar lafiya ta ƙasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Abuja, babban birnin Najeriya.
A cewar jami'ar, gwamnati ta sanar da ƙudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar ƙoda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a ɓoye.
Ta ce "ma'aikatar ta yi tir da irin wannan mummunar ɗabi'a ta safarar ƙoda kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.
Ma'aikatar lafiyar ta kuma tunatar da mutane game da sashe na 51 zuwa 56 na dokar lafiya ta ƙasa da ya haramta safarar ƙodar.
"Mutanen da suka ƙi bin dokar sun aikata laifi kuma za su iya fuskantar biyan tarar naira miliyan ɗaya ko zama gidan yari ko ma duka biyun.











