Bashin da ake bin United ya kusan kai fan biliyan daya

An wallafa

Bashin da ke kan Manchester United ya kai £969.6, idan aka hada da na banki da na biyan sayen 'yan kwallo da ta yi.

Kungiyar Old Trafford ta bayyana kididdigar kudi na zango na biyu zuwa 31 ga watan Disamba, kamar yadda ta sanar ranar Alhamis.

Kididdigar an yi ne domin fayyace kadarar kungiyar, don inganta Old Trafford da filin atisaye na Carrington.

Ta tabbatar da cewar bashin da ke kan kungiyar ya karu.

Uwar bashin da ake bin United ya kai dalar Amurka $650m, idan ka sauya kudin ya kai £535.7m idan ka kwatanta da £477.1m a irin wannan matakin a bara.

Kungiyar ta kara karbar bashin £206.2m da kuma kudin 'yan wasan da ta saye da ake bin ta bashi ya kai £227.7m.

Kungiyar tana da kudi a hannu £31m ko makamancin haka.

An sanar da BBC cewar kididdigar ta fayyace huldar kudi da United ke yi, koda yake tana ganin sauyi, wadda ke samun makuden kudi a nuna wasanninta a talabijin da masu shiga kallo a sitadiya da take tsammani zai karu.

Sai dai United ta ce ta ci ribar £6.3m, kuma kudin tallace-tallace ya karu zuwa kaso 43.2 cikin 100 wato £50.4m.

Ta kuma ce ta samu wannan ci gaban bayan kulla yarjejeniyar tallata kayanta da Tezos.

Albashi ya yi kasa zuwa £20.4m kenan kaso 20.9 cikin 100, bayan da kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ba ta buga Champions League a kakar nan.

United wadda ta lashe Caraboa Cup a bana tana ta uku a Premier League mai kwantan wasa biyu, bayan da za a fara karawar mako na 29 a makon nan.

United za ta buga daf da karshe da Brighton a FA Cup, sannan ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a Europa za ta fafata da Sevilla gida da waje.