Haaland ya ci kwallo hudu rigis ya kara matsi a kan Arsenal

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester City ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier da tazarar maki daya tsakani da Arsenal, bayan doke Wolverhampton 5-1 ranar Asabar a Etihad.

Erling Haaland ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti a minti na 12 da fara tamaula, sannan ya kara na biyu a minti na 35, sai ya ci na uku daf da hutu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Haaland ya zura na hudu a raga, sannan Julian Alvarez ya kara na biyar.

Wolves, wadda ta yi nasara 2-1 a wasan farko a Molineux a bana ta farke daya ta hannun Hee-Chan Hwang a zagaye na biyu.

Tsohon dan wasan Borussia Dortmund, ya zama na uku da ya ci kwallo uku rigis a wasa biyu tun kan hutu, wanda ya yi wannan bajintar a kan Nottingham Forest a bana.

Wadanda suka fara kafa tarihin sun hada da Andrew Cole na Manchester United da kuma Micheal Owen na Liverpool.

Wannan shi ne karo na 30 da aka ci kwallo uku rigis a Etihad, shi ne filin da yake kan gaba a yawan zura uku rigis a raga a wasanni da yawa.

A ranar Asabar Arsenal ta doke Bournemouth 3-0 a wasan mako na 36 a Emirates kenan ta ci gaba da zama ta daya da maki 83.

Ita kuwa City mai kwantan wasa tana ta biyu da maki 82, mai rike da kofin Premier League na bara.

Ranar Lahadi 12 ga watan Mayu, Arsenal za ta je Manchester United, domin buga wasan mako na 37 a Old Trafford a Premier League.

Tun kafin nan ranar Asabar 11 ga watan Mayu, Manchester Ciity za ta je gidan Fulham a dai gasar ta Premier League.