Hanyoyi uku da Trump ke ƙoƙarin bi don kawo wa Kamala Harris cikas

Trump and Harris

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A daidai lokacin da ake ta kai ruwa rana a tarihin siyasar Amurka wanda kuma ba a taɓa ganin irin sa ba, a ɓangare guda Kamala Harris na samun hanya mai sauki ta shimfiɗa manufofinta. Ko da yake watakila hakan ba zai ɗore ba.

Tony Fabrizio, mai kuri'ar jin ra'ayin jama'a na Donald Trump, ya kira batun da ke faruwa a siyasar ƙasar da "Harris Honeymoon" - inda haɗakar ƴan jarida da kuma karfin iko suka haɗu don bai wa 'yan jam'iyyar Democrat damar samun cigaba.

Abin da ya shafi hutun amarci, shi ne ya kan zo ƙarshe. Haƙiƙanin rayuwar aure, ko kuma a wannan yanayin dangantakar da ke tsakanin Ms Harris da jama'ar Amurka masu jefa ƙuri'a, na da hanyar sake tabbatar da kanta.

Ƴan jam'iyyar Republican sun yi ta mayar da martani bayan sanarwar da Mista Biden ya yi na janye wa daga neman takarar shugaban ƙasa.

Ga wasu ɓangarori uku da ake ta sukar jam'iyyar Democrat - da kuma hanyoyi da jam'iyyar za ta bi wajen kawar da su.

...

1. Kiran Harris da 'mai ra'ayin riƙau'

Abubuwan da Ms Harris ta yi a lokacin yakin neman zaɓen shugaban kasa na jam'iyyar Democrat a 2020 na nan cikin zukatan mutane.

Abubuwan sun hada da rashin gamsasshen saƙo, yaƙin neman zaɓe tare da rashin jituwa a cikin gida da ɗan takarar da ke da saurin yin kra-kurai lokacin tattaunawa.

Wani abu kuma ya faru a lokacin takarar shugaban ƙasa na tsohuwar ƴar majalisar dattawan. Ita - kamar sauran mutane da yawa daga cikin 'yan takarar a waccan lokacin - ta kasance mai ra'ayin rikau, don yin daidai da masu jefa ƙuri'a na Democrat.

Matt Bennett, mataimakin shugaba kan harkokin jama'a a Third Way, wata cibiyar tunani ta Demokradiyya ya ce "An samu matsin lamba mai yawa kan waɗannan mutanen daga wajen masu fafutuka." "Lokacin da kuke fafatawa a zaɓen fidda gwani, abubuwan da kuka fi so a siyasance sun sha bamban kafin zuwa karshen babban zaɓe."

Tsawon shekarar 2019 - a cikin muhawara da tattaunawa - Harris ta amince da soke inshorar lafiya na masu zaman kansu don tsarin gwamnati. Ta yaba da garambawul na aikin ‘yan sanda, gami da mayar da kasafin kuɗin aiwatar da doka zuwa wasu muhimman abubuwa.

Biden and Kamala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan, Kamala Harris ce tare da Bernie Sanders da Joe Biden a wajen muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa da aka shirya a 2019

Ta amince da soke dokar shiga Amurka ba tare da izini ba kuma ta yi jin daɗin kawar da hukumar shige da fice da tilasta bin doka. Ta goyi bayan dokar kare muhalli kuma ta goyi bayan haramta hako mai a bakin teku.

Yanzu waɗannan abubuwa za su iya dawowa su kawo mata cikas.

...

2. Kowane irin nasara mai kyau ko mara kyau, zai shafi Kamala

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuri'u sun nuna cewa yaƙin neman zaɓen Biden na fuskantar kalubale a tsawon watanni. Mutane ba su karɓi tsare-tsarensa na shige da fice ba. Duk da cewa an samu raguwar hauhawar farashi kuma tattalin arziki na girma, masu zaɓe na ɗora alhakin tashin farashin kayayyaki a kan shugaban.

Goyon baya da yake bai wa Isra'ila a yaƙinta da Gaza, ya sanya farin jininsa da kuma goyon baya na raguwa a wajen matasa masu zaɓe.

Ms Harris, a matsayinta na mataimakiyar shugaban ƙasa, za ta shiga cikin sahun kowane irin yanayi da aka kwatanta gwamnati mai ci - ko da mai kyau ko mara kyau.

Tuni ƴan jam'iyyar Republican suka tsaya mata a kan wuya da batun masu shige da fice, inda suke kiranta da mai kawo cikas a kan iyaka - wani abu kuma da kafafen yaɗa labarai ma ke amfani da shi wajen bayyana ta .

"An fi sanin Kamala Harris a matsayin wadda ta gaza kuma mataimakiyar shugaban ƙasa da ba ta karɓu wajen jama'a ba wadda kuma ta juyawa mai gidanta baya don samun tikitin tsayawa takarar da ba ta cancanta ba, amma masu zaɓe za su koyi darasi, idan abubuwa suka taɓarɓare," a cewar Taylor Budowich, wanda ke gudanar da wani kwamiti da ke da alaƙa da yakin neman zaɓen Trump.

Zaɓen Amurka

Asalin hoton, Getty Images

A cewar Mista Benneth, Kamala ba za ta iya nesanta kanta daga irin nasarori da Biden ya samu ba, sai dai za ta iya fito da su ta hanya mai kyau domin faranta wa masu zaɓe, duk da irin sukar da take sha wajen ƴan Republican.

...

3. Sukar lokacin da take mai shigar da ƙara

A kuri'ar jin ra'ayin jama'a na farko na yakin neman zaɓenta na shugaban ƙasa, Ms Harris ta yi wani batu na sukar tsohon shugaban ƙasa. Ta bayyana cewa ta kasance mai shigar da ƙara a kotu da kuma babban attoni janar na jihar California, inda ta ce ta ga masu aikata laifi daban-daban.

"Don haka ku saurare ni idan na ce na san mutane irin Donald Trump," ta karkare da cewa.

Craig Varoga, wani mashawarcin a kamfen ɗin Domocrat kuma mai koyarwa a Jami'ar Amurka, ya kira mataimakiyar shugabar kasan mai bin doka da oda - wanda ba ta samu ikon amfani da shi kan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar Democrat a 2019, lokacin da garambawul ɗin aikin 'yan sanda ya kasance babban batu.

Sai dai tuni yaƙin neman zaɓen Trump ya fara nuna alamun yadda za su mayar da martani. Manajan yaƙin neman zaɓensa, Chris LaCivita, ya juya wa wani ɗan takarar jam'iyyar Republican baya, wanda kuma ake zaton yana da karfin iko.

A 2004, ɗan takarar Democrat John Kerry yana yin la'akari da tarihinsa a matsayin tsohon sojan Yakin Vietnam da aka karrama, a matsayin hujjar cewa zai zama babban kwamanda a lokacin yaƙin Iraki.

Mista LaCivita ya jagoranci jerin tallace-tallacen na ɓata wani da ke nuna shakku kan kishin kasa da jaruntakar Mr Kerry, inda ya nuna ma'aikatan ruwa da suka yi aiki tare da Kerry a cikin wani jirgin ruwa mai sauri na sojojin ruwa da ke sintiri a koguna da gaɓar teku a Vietnam.

...

Kallon da za a riƙa yi wa Harris

A wani rubutu da ya yi, Mista Fabrizio ya ce Kamala Harris "ba za ta iya canza waye ita ba ko kuma abin da ta yi". Ya ce nan ba da jimawa ba masu zaɓe za su fara kallonta a matsayin "mai alaƙa da Mista Biden" kuma za su gano manufofinta mara kyau.

A gefe guda, Ms Harris da yakin neman zaɓenta za su yi aiki wajen bayyana waye ita ƴar takarar kuma menene maufofinta.

Hanya ɗaya da za su iya yin hakan, a cewar Mista Varoga, shi ne zaɓar mataimakin shugaban ƙasa.

"Wannan ne mataki na farko da ɗan takarar shugaban ƙasa zai yi domin mutane da ke can waje za su gani," in ji shi. "Hakan zai bai wa mutane damar sanin wane irin makoma za ta samar musu."

Duk mataimaki za ta ɗauka, zai bai wa masu zaɓe su san wane irin shugabanci za ta yi.

A makonni masu zuwa, ƙoƙarin gano waye Kamala Harris - ta hanyar kalamanta, kuri'unta da kuma yakin neman zaɓenta na baya - zai kwatanta irin kallon da mutane za su riƙa yi mata idan suka shiga rumfunan zaɓe a watan Nuwamba.

Hakan zai kuma gano cewa ko karewar hutun amarci zai kasance mara daɗi ga jam'iyyar Democrat ko kuma zai ci gaba har na tsawon shekara huɗu masu zuwa.