'Ƴan uwana 19 ne suka mutu a girgizar ƙasar Afganistan'

Bayanan bidiyo, 'Na rasa ƴan uwana 19 a girgizar ƙasar Afganistan'
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fiye da mutum 1,000 ne suka mutu bayan wata girgizar ƙasa mai maki 6.1 da ta shafi gabashin Afghanistan a ranar Laraba.

Likitoci a yankin sun shaida wa BBC cewa yara da dama sun mutu.

Wata wadda ta rayu a asibitin yankin Patkika ta ce ta rasa mutum 19 a cikin danginta.

Girgizar ƙasar ita ce mafi muni da ta faru a cikin shekaru 20 da suka gabata kuma babban ƙalubale ne ga ƙungiyar Taliban, wacce ta ƙwace iko da ƙasar a bara.

Hukumomi a Afghanistan na neman taimakon ƙasashen duniya don shawo kan bala'in.

Afghanistan tana fuskantar bala'o'i da kuma matsalar tattalin arziki, kuma wani babban jami'in Taliban Abdul Qahar Balkhi, ya ce gwamnati ba ta da kuɗin da za ta iya taimakon mutane yadda ake buƙata.