Wane ne sabon sarkin Dutse?

Asalin hoton, Twitter/madachi_abba
A yau ne gwamnatin jihar jigawa da ke arewacin Najeriya ta bayyana naɗin Hameem Nuhu Muhammad sunusi a matsayin sabon sarkin masarautar Dutse a jihar, bayan rasuwar tsohon sarkin Nuhu Muhammadu Sunusi.
Marigayi Nuhu Muhammadu sunusi ya rasu ne a makon da ya gabata a wani asibiti da ke Abuja babban birnin ƙasar sakamakon fama ra gajeren rashin lafiya.
Gwaman jihar Jigawa Muhammad badaru Abubakar ne ya sanar da naɗin Hameem Nuhu Muhammad Sunusi a matsayin sabon sarkin Dutsen ranar lahadi da rana.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar wa da BBC naɗin ranar Lahidi da rana.
Ya ƙara da cewa masu zaɓen sarki ne suka kai wa gwamna sunayen masu neman saurautar uku, inda shi kuma gwamna ya tabbatar da Hameem wanda ɗa ne ga marigayin a matsayin sabon sarkin.
Kwamishinan ya ce mutam ukun da aka kai wa gwamna sunayensu sun haɗar da Galadiman Dutse, da Wamban Dutse da kuma shi Hameem wanda shi ne Ɗan Iyan Dutse kafin naɗin nasa.
Nan gaba kaɗan ne kuma masarautar za ta sanar da ranar da za ta yi bikin naɗin sabon sarkin.
Tarihin sabon sarkin
Am haife shi a ranar 26/2/1979. Kuma shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Dutse Nuhu Muhammadu sunusi.
Ya yi makarantar firamare a makarantar 'ya'yan sojojin sama da ke Kano. Daga nan ya fara karatun sakandare a Crescent International School amma bayan shekara biyu ya koma kwalejin gwamnatin tarayya ta Kano (FGC Kano) a inda ya kammala karatun sakandaren.
Ya yi karatunsa na digiri a fannin kwamfuta a Jami’ar Monash ta ƙasar Australia reshen Malaysia.
Bayan nan ne kuma ya yi digiri na biyu a fannin kasuwanci, wato MBA, a Jami’ar Nottingham Trent, a Malaysian.
Gogewar aiki
Ya yi aiki na shekara ɗaya a kamfanin Marcus Evans Consulting na Malaysia a matsayin jami’in kasuwanci
Sannan kuma ya koma aiki a Bilyak Consulting a matsayin mai kula da sashen haɓaka kasuwancin kamfanin daga 2007 zuwa 2011.
daga baya kuma ya koma kamfanin SMD Consulting daga 2011 zuwa 2016 inda ya zama jami’in kula da yankin Arewacin Nigeria na kamfanin.
Ya zama Babban Darakta na kamfanin MHS Energy Limited daga shekara ta 2016 har lokacin da ya zama Sarkin Dutse.
Muƙaman da ya riƙe
Kafin naɗin nasa a matsayin sabon sarkin Dutse, Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya riƙe sarautar Sarkin Dawakin Tsakar-Gida da kuma Ɗan Iyan Dutse.
Kuma sabon sarkin shi ne shugaban kamfanin gine-gine na MHS Engineering.
Iyalansa
Sabon sarkin Hameem Nuhu Muhammad Sunusi na da mata ɗaya da 'ya'ya biyu












