Real ta fara shirin tunkarar Man City a Champions League

An wallafa

Real Madrid ta fara shirin karbar bakuncin Manchester City, bayan da ta lashe Copa del Rey ranar Asabar.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta doke Osasuna 2-1 ta lashe Copa del Rey na 20 jimilla.

Ranar Talata Real Madrid za ta kece raini da Manchester City a karawar farko a daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu.

Hakan ya sa Real ta koma atisaye nan take, inda wadanda suka buga wasan karshe da Osasuna suka motsa jiki a rufaffen daki daga baya suka shiga fili suka yi tsalle-tsalle.

Sauran 'yan wasan kuwa suka ci gaba da atisaye a cikin fili da guje-guje, daga baya suka koma gwada gola da yin fasin a tsakaninsu.

Shi kuwa Mendy ya yi atisaye tare da 'yan wasa a kokarin da yake na komawa kan ganiya, Ceballos ma na fatan murmurewa a atisayen da yake yi.

Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Chelsea, tun kan nan ta yi nasara a kan Liverpool.

Ita kuwa City ta kawo wanna matakin, bayan da ta fitar da RB Leipzig da Bayern Munich.

Real Madrid ita ce mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla, ita kuwa City ba ta taba lashe kofin ba.

Sai dai Guardiola ya ci kofin Champions League biyu a Barcelona, wanda ya kasa dauka a Bayern Munich da kuma kungiyar Etihad da yake jan raga.