Waiwaye: Barazanar gwamnati da rikidewar zanga-zanga zuwa tarzoma

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Ƴansanda a Kano sun baje kolin waɗanda aka kama lokacin zanga-zanga

kano

Asalin hoton, POLICE COMMAND KANO

Rundunar ƴansanda a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama mutum 326 bisa zargin su da hannu a yamutsin da aka samu lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a ranar Alhamis.

Rundunar ta ce cikin mutanen da ta kama akwai mata, da maza da kuma ƙananan yara.

Haka nan sun bayyana cewa an ƙwace bindiga ƙirara AK47.

Zanga-zangar lumanan da matasa suka shirya a faɗin ƙasar ta rikiɗe zuwa rikici a wasu jihohi, lamarin da ya kai ga sanya dokar ta ɓaci a jihohi biyar.

An tarwatsa masu zanga-zanga a gidan gwamnatin Kano

masu zanga-zanga a Kano

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, dubban matasa a jihar Kano sai kara fitowa suke daga unguwanni suna taruwa a kan titin gidan gwamnati.

Wakilin BBC a Kano ya ruwaito cewa matasan rike da alluna suna ta furta kalmomin "Ba ma yi" inda ya ce wasu matasan na komawa gida suna sake shiri.

A cewarsa, ana fargabar an harbi mutum uku cikin masu zanga-zangar.

A daina yi wa masu shirin zanga-zanga barazana - Amnesty

Janar CG Musa

Asalin hoton, DEFENCE HQ/X

Gabanin zanga-zangar ta neman gwamnati ta yi maganin matsalolin da ke addabar 'yan Najeriyar na matsin tattalin arziki da tsaro da kuma shugabanci, wadda aka fara ranar, Alhamis 1 ga watan Agusta, hukumomin Najeriya sun yi gargadi ga masu shirya zanga-zangar kan abin da za ta iya haifarwa.

Wannan ya sa kungiyar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Amnesty International ta mayar da martani da cewa yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ba tsari ba ne na dimokuraɗiyya.

Yekuwar zanga-zangar ta samu karbuwa a shafukan sada zumunta da kuma wasu ‘yan kasar.

Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗin ne da cewa zanga-zangar da za ta iya jefa ƙasar cikin tashin hankali tare da yin kwatanci da halin da ƙasashe kamar Kenya da Sudan da Libya ke ciki sakamakon yin bore.

Harin bam ya kashe mutum ɗaya a jihar Borno

Ma'aikatan agaji

Asalin hoton, NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, Nema, ta bayar da rahoton tashin wani bam a kan babbar hanyar garin Damboa na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Hukumar ta ce dakarunta na kai agajin gaggawa sun gudanar da aikin haɗin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki domin kwashe waɗanda fashewar ta rutsa da su zuwa asibitin ƙwararru na jihar.

An samu rahoton cewa mutum ɗaya ya rasu a hanyar zuwa asibitin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da wani ayarin motocin haya da suka taso daga Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa suka ci karo da bam ɗin da ake zargin ƴan bindiga ne suka dasa.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dagaci a Sokoto

'yanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Isa Bawa tare da ɗansa a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Ahmed Rufa'i ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels afkuwar lamarin, inda ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike.

Wani babban ɗa ga dagacin, Isa Gobir ya ce an yi wa mahaifin nasa kwanton-ɓauna a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa garinsa na karamar hukumar Sabon Birni daga Sokoto.

'Yanbindigar sun kuma yi garkuwa da ƙarin mutum biyar a yankin a ranar da aka ɗauki dagacin, abin da ya sa hankalin jama'ar yankin ya tashi.

An zargi ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan da yi wa mata fyaɗe

mace da lullubi

Asalin hoton, Getty Images

Wani sabon rahoto kan cin zarafi ta hanyar lalata a Sudan ya zargi ɓangarorin da ke rikici da juna da aikata fyaɗe a kan mata da ƴan mata waɗanda shekarunsu ba su wuce aƙalla tara ba a Khartoum, babban birnin ƙasar da kuma biranen Omdurman da Bahri.

Rahoton wanda hukumar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta fitar, ya zargi dakarun RSF da aikata cin zarafi yayin da suke iko da yankunan da ke makwabtaka da juna a birane da dama.

Rahoton ya kuma zargi sojojin da ke mulkin ƙasar da aikata fyaɗe a wuraren da suke iko da su musamman waɗanda suka kwace daga wajen dakarun RSF.

Sai dai dukkan ɓangarorin sun musanta zarge-zargen.

Gwamnatin Najeriya za ta fara sayar wa matatar Dangote ɗanyen mai a Naira

Matatar man Dangote

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara sayar wa matatar Dangote ɗanyen mai a Naira, a wani yunkuri na tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma farashin Dala da Naira.

Gwamnatin ta sanar da haka ne a ranar Litinin bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka gudanar.

Majalisar ta amince da cewa a sayar da mai ganga 450,000 da za a yi amfani da shi a cikin ƙasar a Naira ga matatun Najeriya, ta hanyar fara wa da matatar Dangote.

Matatar Dangote na buƙatar jiragen dakon ɗanyen mai 15 a kan farashin dala biliyan 13.5 duk shekara.