Wane irin martani Iran za ta mayar wa Isra’ila kan kisan shugaban Hamas?

Ismail Haniyeh

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kashe jagoran Hamas, Ismail Haniyeh a ranar Talata sakamakon wani hari ta sama a Tehran
    • Marubuci, Kasra Naji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kisan da aka yi wa shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas zai kara dagula lamurra a zaman tankiyar da ake yi a yankin.

Ismail Haniye ya je Tehran ne domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, inda aka kashe shi ta hanyar wani hari ta sama.

Nan take hukumomin Iran suka dora laifin lamarin kan Iran kuma jagoran addini na Iran, Ayatollah Khamenei ya lashi takobin aiwatar da “tsattsauran mataki“ kan Isra’ila.

"Mun amince cewa nauyin ɗaukar fansar jininsa a kanmu yake kasancewar ya yi shahada ne a Jamhuriyar Musulunci ta Iran," in ji Khamenei.

Ismail Haniyeh da Ayatollah Khamenei

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haniyeh ya gana da jagoran addini na Iran, Ayatollah Khamenei, kwana ɗaya kafin kashe shi

A watan Afrilu, ƙasashen biyu sun kusa gwabza yaƙi bayan da wani harin da Isra'ila ta kai ya kashe wani babban kwamandan Iran a Syria.

A matsayin martank, Iran ta harba daruruwan jirage marasa matuki da rokoki zuwa cikin Isra’ila, wadda ita ma ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan birnin Isfahan na Itan.

Mista Haniye ya rika zirha-zirga zuwa Iran a cikin shekarun baya-bayan nan domin ganawa da jagoran addini na kasar da sauran manyan jami’an gwamnati.

Haniyeh - tare da shugaban kungiyar Islamic Jihad, wadda ita ce kungiya ta biyu a Lebanon da wani babban jagoran yan Houthi sun kasance a sahun gaba a lokacin bikin nadin sabon shugaban kasar.

Kafin nan dukkaninsu sun gana da Ayatollan Khamenei, wanda ya yi kusu kyalkyan tarba.

Yaro ɗan Falasɗinawa ɗauke da fosta da ke ɗuke da fuskar Shuguban Hamas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Falasdinawa da dama a sansanin yan gudun hijira da ke Beirut a Lebanon sunyi zanga-zangar nuna adawa da kisan shugaban siyasar Hamas.

Iran ta ce an kashe Haniye da dogarinsa a wani gidan saukar baki a Tehran sa misalin karfe 02:00 na dare agogon Iran ta hanyar wata harba wani makami daga wajen kasar ta Iran.

Iran ta yi yakinin cewa Isra’ila ce ta ke da alhakin kashe wani masani kimiyyar nukiliya ta Iran a shekaru goma da suka wuce amma kuma a baya ba su taɓa harin wani mai martaba ko shugaba ba.

Kisar dai za ta zo a ni matsayin wani abu mai ban kunya ga Iran kuma ya dasa ayar tambaya ka ƙarfi da iyawar hukumar tsaronta.

Shekaru uku da suka gabata, tsohon ministan tattara bayanan sirri , Ali Younesi ya ce kutsawar Isra`ila a Iran yayi tsananin suka fara takatsatsan da rayuwarsu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin jami`an tattara bayanan siiri na Iran suka yi iƙirarin cewa suna tarwatsa hanyoyin sardarwa na Isra`ila a Iran

Mene ne abu na gaba?

Abun da aka fi damuwa da shi a yanzu shine martanin Iran da kuma yadda za ta zo da kuma ma`anar martanin ga fargaba a yankin.

Kisar Haniyeh ya zo ne sa`o`i kaɗan bayan da Isra`ila ta yi iƙiranin kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandan sojojin Hezbollah na Lebanon a kudancin Beirut, abin da ya ƙara ba su dalilin ƙara girman yaƙi da makamai masu linzami a keteran iyaka da Isra`ila.

Iran za ta kuma iya saka mayaƙan sa kai na yankin ƙara ƙaima wajen kai wa Isra`ila hari.

A halin yanzu, akwai masu sharhi a yankin da suka yi yaƙinin cewa fargabar da ke tsakanin Isra`ila da Hezbollah zai kai wani matsayi da ke nuna alamun yuwuwar ɓarkewar cikakkiyar yaƙi tsakaninsu.

Sabon shugaban ƙasar Iran

Bayan mutuwar Haniyeh, Iran ta rantsar da Masoud Pezeshkian a matsayin sabon shugaban Iran inda ya ɗau alwashin inganta huldar diflomasiyya da kasashen waje.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Masoud Pezeshkian

Asalin hoton, @drpezeshkian / X

Bayanan hoto, Ismail Haniyeh
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan nuna goyon bayansa ga Falasɗinawa, Pezeshikian ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankalinta ga ayyukan da zu su amfana ƙasar, da zamar lafiyar duniya ta hanyar hulɗar ƙasashen waje masu jitiwu da daidaito.

Amma kuma sabon shugan ya ce kisan Haniyeh zai zama cikas a shirye-shiryensa.

A matsayin shugaban ƙasa da ke son gyara dangataka da sauran ƙasashen duniya, Iran za ta iya kokwanto wajen kai hari ga Isra`ila.

Amma kuma wannan kisar ya nuna alamun yiwuwar tsagaita wuta da kuma tattaunawar zaman lafiya a yaƙin da yayi sanadin mutuwar sama da Falasɗinawa 38,000 a cewar ma`aiktar lafiyar Hamas.

Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani wanda shine babban mai shiga a tattaunawar tsagaita wuta a rikicin Isra`ila da Hamas ya ce kisar Haniyeh ya kawo cikas ga tattaunawar saboda yana ɗaya daga manyan da ke shiga cikin tattaunawar.

Shin wannan zai haddasa babban yaƙi a yakin? hakan na da wahalar tattancewa. Amma kuma akwai alamun da ke nuna cewa babu wanda yake son hakan a halin yanzu.