Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta lashe Premier na hudu a jere na 10 jimilla
Manchester City ta lashe Premier League na bana na hudu a jere na shida a kaka bakwai na 10 jimilla.
City ta yi nasarar doke West Ham 3-1 a wasan karshe na mako na 38 da suka kara ranar Lahadi a Etihad.
City ta fara cin kwallo ta hannun ta Phil Foden a minti na biyu da take leda na shida da ya zura a raga a bana daga wajen yadi na 18 a kakar bana.
Haka kuma shi ne ya kara na biyu, sannan Rodri ya ci na uku a wasan.
West Ham ta zare daya ta hannun Mohammed Kudus saura minti uku su je hutun rabin lokaci.
Wannan shi ne wasa na 262 da David Moyes ya ja ragamar West Ham United da cin karawa 112 da canjaras 55 aka doke shi 95.
Haka kuma karo na 16 da Moyes ya kasa nasara a kan Pep Guardiola a dukkan fafata da canjaras hudu da rashin nasara 12.
City ta zama ta farko da ta lashe Premier League na hudu a jere, kuma na shida cikin kaka bakwai a tarihin babbar gasar tamaul ta Ingila shekara 135.
City ta lashe kofin bayan wasa 44 a jere a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa da cin karawa 37 da canjaras bakwai.
Ba a doke City ba a wasa 17 da ta kara da West Ham da cin 14 da canjaras uku a gasar ta Premier League.
Kuma West Ham ta yi rashin nasara 16 daga 18 da ta ziayarci Etihad da canjaras daya da rashin nasara daya.
City ta doke West Ham 2-0 a wasan karshe a gasar Premier a 2014, inda Samir Nasri da Vincent Kompany suka ci mata kwallaye ta kuma lashe kofin a ranar.
Pep Guardiola ya lashe kofin lik na 12 a kaka 15 a matakin koci, mai uku a Barcelona da uku a Bayern Munich da shida a Manchester City.
Erling Haaland ya ci kwallo 64 a wasa 66 a Premier League shi ne kan gaba a wannan bajintar a kaka biyu da ya fara buga babbar gasar tamaula ta Ingila.
Haaland ya lashe takalmin zinare karo biyu a jere da kwallo 27 a raga, wanda ya zura 36 a bara a Premier League.
Rodri ya yi wasa 74 ba tare da an doke Manchester City ba, inda aka ci karawa 58 da shi da canjaras 16, tun bayan da Tottenham ta ci 1-0 a cikin Fabrairun 2023.
Bajintar da City ta yi a kakar nan
City ta buga wasa 38 da cin 28 da canjaras 7 da rashin nasara uku da cin kwallo 96 aka zura mata 34 da maki 91.
Phil Foden gwarzon dan wasan Premier League na bana, wanda marubuta labarin wasan tamaula suka zaba a bana..
Foden ya lashe ƙyautar wanda ya ci kwallo 19 ya bayar da takwas aka zura a raga a babbar gasar tamaula ta bana.
City ce kan gaba a yawan cin wasan Premier League, wadda ta yi nasara 28, sai Arsenal ta biyu mai cin karawa 28 da kuma Liverpool mai 24.
Wannan shi ne Premier League na 10 jimilla da Manchester City ta lashe.
Wadanda ke kan gaba a yawan lashe Premier League
- Manchester United 20
- Liverpool 19
- Arsenal 13
- Manchester City 9
- Everton 9
- Aston Villa 7
- Chelsea 6
- Sunderland 6
- Sheffield Wednesday 4
- Newcastle United 4
- Blackburn Rovers 3
- Leeds United 3
- Wolverhampton 3
- Huddersfield Town 3
- Derby County 2
- Tottenham 2
- Burnley 2
- Portsmouth 2
- Preston North End 2
- Leicester City 1
- Nottingham Forest FC 1
- Ipswich Town 1
- West Bromwich Albion 1
- Sheffield United 1