Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutanen da suka samu mafaka a cocin Gaza 'na cikin fargaba'
- Marubuci, Oliver Slow
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Fararen hular da suka maƙale don neman mafaka cikin wata coci a Birnin Gaza na raye cikin firgici, kamar yadda 'yan uwansu suka tabbatar.
Fifi Saba, wadda 'yar uwarta ke fakewa cikin cocin Holy Family Church, ta ce mutane na fargabar za a harbe su idan suka fita daga cocin.
A ranar Asabar da ta gabata wani sojan harbi daga nesa na Isra'ila ya harbe wata uwa da 'yarta a cocin, a cewar ikilisiyar Latin Patriarchate of Jerusalem.
Fafaroma Francis ya yi tir da harin, har ma ya kira shi da "ta'addanci".
"Uwar, Mrs Nahida Khalil Anton, da 'yarta Samar Kamal Anton, maharba sun kashe su, kuma suka raunata wasu lokacin da suke ƙoƙarin shiga banɗaki," kamar yadda ya bayyana ranar Lahadi.
"Wasu na cewa 'Wannan ta'addanci ne. Wannan yaƙi ne.' Tabbas yaƙi ne. Ta'addanci ne," in ji shi.
Ms Saba, mai bin ɗariƙar Katolika kuma mazauniyar Amurka a yanzu, ta faɗa shirin Today na BBC Radio 4 cewa tana cikin damuwa game da 'yar uwarta, da ɗn uwanta, da surikinta da kuma 'ya'yansu biyu masu shekara 9 da 12, waɗanda aka tarfa a cikin cocin.
Ta ce tana samun labarai game da su ta hannun wani ɗan uwansu, wanda ke samun damar yin magana da 'yar uwar tata sau ɗaya a rana.
"An kulle su a ciki," in ji ta. "Ba su iya ganin waje sosai, kuma kusan ba su san abin da ke faruwa a sauran duniya ba. Ba su da waya, babu intanet, babu labarai."
Ta ce 'yar uwar tata kan tambayi abin da ke faruwa a waje, yayin da suke jin rugugin bama-bamai a saman kansu.
"Fargabar da suke ciki kamar gaske ba," in ji ta.
"Na gano wata rana lokacin da take bayyana yanayin a matsayin mai wuyar gaske tana nufin ta shaida kisan mutum biyu - matan nan biyu a cikin cocin," kamar yadda Ms Saba ta faɗa.
Ta ƙara da cewa mutanen sun shafe awanni suna kwance a dandariyar ƙasar cocin, saboda "sun fahimci cewa Isra'ilawan na harbin duk wani abu da suka ga ya motsa".
"A tsorace suke su je banɗaki saboda an harbi matan ne lokacin da suke zuwa banɗaki," a cewarta, tana mai cewa an yanke ruwa daga cocin tsawon wasu kwanaki.
Abinci ma ya yi ƙaranci, in ji ta, inda mutanen ke cin dafaffiyar taliya tsawon sati uku.
"Ina jin 'yan kwanakin da suka wuce ba su da abinci," a cewarta.
A ranar Asabar, ikilisiyar Latin Patriarchate of Jerusalem ta ce an harbe Kiristoci biyu mata - Nahida da 'yarta Samar - lokacin da suke shiga wani gini a farfajiyar cocin da ake kira Sister's Convent.
"An harbe ɗaya ne lokacin da take ƙoƙarin ceton ɗayar," a cewar wata sanarwa. An harbi wasu mutum bakwai kuma aka raunata su "lokacin da suke kokarin kare sauran a cikin cocin" ranar Asabar.
Ikilisiyar ta ce ba a yi wani gargaɗi ba kuma ta ƙara da cewa: "An yi musu kisan gilla a cikin farfajiyar, wurin da babu wasu mayaƙa."
Ta ce tun da farko a ranar Asabar wata tankar Isra'ila ta buɗe wuta a kan wani ɓangare na cocin, inda masu buƙata ta musamman 54 ke ɓuya. Hakan ya haddasa gobarar da ta lalata injin lantarki na ginin wanda shi kaɗai ne ke ba da wuta, kuma wasu daga cikin mutanen ba za su iya amfani da na'urorin nimfashinsu ba, in ji sanarwar.
A martanin da ta mayar kan wasiƙr, rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce "tana ɗaukar batun kai wa wurare masu muhimmanci hari da da muhimmancin gaske".
Ta ce wani lamari ne ya faru da dakarunta a yankin Shejaiya, kuma wai bincikensu ya nuna cewa sojojin na faɗa ne da mayaƙan Hamas "da suka gano a kusa da cocin".
"IDF na gudanar da cikakken bincike kan lamarin," in ji ta.
BBC ta tuntuɓi IDF don jin ƙarin bayani game da zarge-zargen kai hari kan mai tsautsayi.
Babu tabbas game da dalilin da ya sa ake kai wa cocin hari, amma Ms Saba ta ce ba ta jin mayaƙan na ciki, kuma 'yar uwarta ba ta yi magana kan zamansu a ciki ba.
"Mun ga yadda cikin kwana uku aka kai wa asibitoci hari, an kai wa makarantu hari, ɗakunan karatu ma haka, kasuwanni ma ba su tsira ba, an kai wa gidajen burodi hari."
Layla Moran, wata 'yar majalisar Birtaniya, ta faɗa wa BBC ita ma cewa akwai waasu 'yan uwanta Kiristocin Falasɗinu da suka maƙale a cocin, bayan sun nemi mafaka sakamakon rushe gidansu a satin farko na yaƙin.
"Yanzu ba ni da wani tabbas ko za su tsira zuwa Kirsimeti," in ji ta, tana mai cewa yanzu ba su da ruwa da abinci.
'Yan uwan nata sun ce sojoji sun shiga farfajiyar cocin kwana ɗaya kafin lokacin kuma suka karɓe iko da wani ɗaki a wani gini.
Mutanen sun aiko da wani hoto da BBC ta gani, na gawar mutum biyu kwance a wajen cocin. 'Yan uwan Moran sun ce gawarwakin na ruɓewa tsawon kwanaki.
"Da alama wannan kawai na nuna yadda Isra'ila ba ta ɗauki kare fararen hula da muhimmanci ba," in ji ta.
Isra'ila na cewa tana kai hare-hare a Gaza ne da zimmar kawar da Hamas kwatakwata, da ceto mutanenta da ake garkuwa da su tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, da kuma cewa ba ta kai wa fararen hula hari.
Sai dai ma'aikatar lafiya a Gaza ƙarƙashin ikon Hamas ta ce Isra'ilar ta kashe mutum kusan 20,000 tare da raunata wasu 50,000 tun daga fara yaƙin.