Man United ta kai kwata fayinal a Europa bayan ruwan ƙwallaye a ragar Socieded

Bruno Fernendes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta kai zagayen kwata fayinals a gasar zakarun Turai ta Europa League, bayan ta yi ruwan ƙwallaye 4-1 a ragar Real Socieded a wasa na biyu na zagayen 'yan 16.

Bruno Fernandes ne ya ƙwallo uku rigis a filin wasa na Old Trafford, cikinsu har da bugun finareti biyu.

Sai dai Mikel Oyarzaba ne ya ciwo mai 'ya'ya daga bugun finareti tun a farkon wasan bayan Matthijs de Ligt ya yi masa ƙeta.

United ta farke minti shida bayan haka ta ƙafar Fernandes, sannan ya sake cin wani finaretin minti biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kafin ya ƙara ta ukun a minti 87.

Diago Dallot ne ya rufe taron da ƙwallonsa ana gab da tashi.

Yanzu Man United za ta fafata da Lyon ta Faransa a zagayen kwata fayinals ɗin, wanda za a fara bugawa a ranakun 10 da 11 ga watan Afrilu.